1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'amala tsakanin Faransa da Jamus

January 22, 2013

Ƙasashen biyu na gudanar da bukukuwan zagayowar cikkar shekaru 50 da rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya tsakanin Jamus da Faransa bayan yaƙin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/17Ovn
German Chancellor Angela Merkel and French President Francois Hollande speak during a meeting with some 200 German and French students and pupils as part of celebrations of the 50th anniversary of the Elysee Treaty, in the Chancellery in Berlin, January 21, 2013. REUTERS/Kay Nietfeld/Pool (GERMANY - Tags: POLITICS)
50 Jahre Élysée-VertragHoto: Reuters

Yanzu haka shugaban Faransa da wata tawagar 'yan majalisun ƙasar suna yin ziyara a birnin Berlin inda ake ci gaba da yin shagulgulan waɗanda zasu kai ƙololuwar su a yau talatawanda ke yin tuni da yarjejeniyar da suka cimma tun a ranar 22 ga watan Oktoba na shekarun 1963.

Ƙara ƙarfafa hulɗa tsaro tsakanin ƙasashen biyu

Shugabannin biyu wato Angela Merkel da Francois Hollande tun da farko sun kasance a tsakiyar wasu matasa kusan guda ɗari biyu waɗanda suka riƙa yi masu tambayoyi a kan al'amura siyasar ƙasasahen guda biyu da kuma hulɗa da dankantar da ke tsakanin su.Da ya ke magana shugaban na Faransa Francois Hollande ya yi tuni da lokacin yan mazan jiya dangane da zamnan doya da man ja da aka kwashe dogon lokaci ana yi tsakanin Jamus da Fransa wanda ya ce wa ya yi tsamani a yau za a samu hulɗa da cuɗanya tsakanin Jamus da Faransa harma akan sha'anin tsaro bayan yaƙi duniya na biyu wanda a yau har a kwai wata runduna ta haɗin gwiwa tsakanin sojijn Jamus da Faransa;amma ya ce duK da haka a kwai buƙatar ƙara ƙarfafa hulda ta tsaro da ma sauran fanoni.Ya ce ''za mu iya yin aiki tare domin ƙara ingata hulɗa ta taro s, ya ce ina ganin tsarin bai ɗaya na al'muran tsaro tsakanin ƙasashen mu na samun ci gaba amma dai ba da sauri ba''.

Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU, M) und Frankreichs Staatspräsident Francois Hollande (links neben Merkel) treffen am 21.01.2013 in Berlin im Rahmen der Feierlichkeiten zum 50. Geburtstag des Elysee-Vertrags 200 deutsche und französische Studenten, Auszubildende und junge Berufstätige im Bundeskanzleramt. Foto: Kay Nietfeld/dpa
Angela Merkel da Francois HollandeHoto: picture alliance / dpa

Tunawa da tarihin yarjejeniyar ga shugabannin ƙasahen biyu

A lokacin muhawara shugabannin biyu su dukanin su sun jadada cewa ƙara dagewar yan siyasa a kan al'amuran ita ce ka ɗai kwai hanyar ma fi a a'ala da zata sa ƙasashen nahiyar Turai sun tsallake matsalolin tattalin arziki da suke fama da su da kuma rashin aikin yi na jama'a galibi matasa.Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ta ke yin jawabi ta yi tuni da irin kalamun da tsohon shugaban na Jamus Konrad Adenauer ya yi amfani da shi;a lokacin da aka saka hannu akan yarjejeniyar tsakaninsa da janar Charles Degaule na Faransa .Ta ce ''Konrad Adenauer a ko wane loaci aka ambato batun hulɗaR tsakanin Jamus da Faransa bayan yaƙi duniya na biyu ya na kwatamta ta da tamkar icen bishiya wanda ya ce kafin a ci moriyarsa inda an dasa shi, to kam za a sha wuya, ta ɗawainiya , ta ce a yau ina ganin an cimma gaci akan wannan al'amari da ya zama amintaka mai ƙarfi tsakanin kasahen biyu''.

German President Joachim Gauck and French President Francois Hollande (C) inspect a guard of honour during a welcome ceremony at the presidential Bellevue palace in Berlin January 22, 2013, during a day of celebrations marking the 50th Anniversary of the Elysee Treaty. REUTERS/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS ANNIVERSARY)
Joachim Gauck shugaban ƙasar Jamus da Francois Hollande na FaransaHoto: Reuters

Shugabannin sun washe kusan sao'i 2 daga bisanni suna tattauna rikicin Mali sannan kuma da babbar ganawar da aka shirya yi tsakanin shugabannin ƙungiyar Tarrayar Turai a nan gaba akan maganar kasafin kudi na shekarun 2014 zuwa 2020 na nahiyar.An shirya a yau shugabannin zasu yi jawabi a gaban ɗaruruwan yan majalisun dokoki na Faransa da Jamus a bukukuwan wannan yarjejeniya ta zaman lafiya wadda ke cikka shekaru 50 a yau.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi