Maaikatan majamia sun kawo nakasu ga aikin ceto a Najeriya | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maaikatan majamia sun kawo nakasu ga aikin ceto a Najeriya

A cewar Jami'an hukumar NEMA mai ba da gajin gaggawa a Najeriya sun sami cikakkun bayanai daga bangaren ma'aikatan cocin, da fara aikin ceto da wuri da an samu raguwar rasa rayuka a ruftawar ginin na jihar Legas.

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta bayyana a wannan Juma'a cewa, masu hidima a majami'a sun kawo cikas na aikin masu agaji na zakulo wadanda suka yi saura cikin baraguzan gini mai hawa shida da ya afkawa mutane da ya yi sanadin mutuwar wasu da dama.

Mafi yawa wadanda suka rasa rayukan nasu sun fito ne daga kasar Afrika ta Kudu, wadanda gwamnatin kasar ta ce al'ummar ta sittin da bakwai sun mutu cikin afkawar ginin, inda mutane sha bakwai kuma suka bace cikin rushewar ginin wanda ke da katafaren shagon cefane a kasa da dakunan karbar baki a sama.

Ibrahim Farinloye, Mai Magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, majami'ar karkashin jagorancin babban malamin na addinin Kirista T.B. Joshua ta rufta ne da misalign karfe 12:44 na ranar Juma'ar da ta gabata, amma ba a bariba maaikatan agaji sun shiga gudanar da ayyukan agaji se bayan karfe biyar a ranar Lahadi, saboda wasu hadiman cocin sun hana maaikatan agajin su gudanar da aikin su yadda ya dace duk kuwa da cewa sun isa inda lamarin ya auku tun da misalin karfe 1:50 na yammaci a ranar ta Juma'a.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo