Ma′aikatan kiwon lafiya a Guinea na kokarin shawo kan cutar Ebola | Labarai | DW | 24.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma'aikatan kiwon lafiya a Guinea na kokarin shawo kan cutar Ebola

Kawo yanzu mutane kusan 60 daga cikin sama da 80 da suka kamu da cutar ne suka rasu a kasar ta Guinea da ke yankin yammacin Afirka.

Gwamnatin kasar Guinea ta sanar a wannan Litinin cewa kwayoyin cutar da aka gano daga mutane uku da aka yi zaton na cutar Ebola ne, kuma suka kai ga kashe mutane biyu a Konakry, babban birnin kasar, ba kwayoyin cutar ta Ebola ba ne. Sakoba Keita babban jami'in sashen yaki da yaduwar cuta a ma'aikatar kiwon lafiya ta Guinea, ya ce cibiyar binciken kwayoyin cuta a birnin Dakar na kasar Senegal ta yi aikin gaggawa tsawon dare a kan kwayoyin cutar daga Konakry, kuma a karshe ba a gano wata kwayar Ebola a cikinsu ba. Hakan ya tabbatar cewa babu Ebola a birnin Konakry, in ban da wani zazzabi da har yanzu ba a gano musabbabinsa ba. Yanzu haka dai jami'an kiwon lafiya da ma'aikatan agaji suna kokarin shawo kan cutar ta Ebola wadda kawo yanzu ta yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 60 a kasar ta Guinea da ke yammacin Afirka.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe