Ma′aikata 900 sun makale a karkashin kasa | Labarai | DW | 01.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma'aikata 900 sun makale a karkashin kasa

Fiye da masu aikin hakar ma'adanai 900 ne suka makale a wajen hakar ma'adanan zinare a lardin Free State na Afirka ta Kudu inda suke can karkashin kasa da misalin zurfin mita 700 zuwa 2,200.

Südafrika illegale Goldmine bei Soweto, Johannesburg (picture-alliance/dpa/K. Ludbrook)

Aikin hakar ma'adanai na cike da hadari a Afirka ta Kudu

Masu aikin hakar ma'adanan sun makale ne a karkashin kasa tun a ranar Laraba saboda daukewar hasken wutar lantarki kamar yadda kungiyar ma'aikatan ta (AMCU) ta bayyana inda ta bukaci masu wurin hakar ma'adanan wato kamfanin Sibanye-Stillwater su gaggauta aikin ceton al'umma.

Kawo yanzu dai an samu damar fitar da masu aikin hakar ma'adanan su 64 amma sama da 900 na karkashin kasa. Shi dai kamfanin Sibanye-Stillwater ya kasance daya daga cikin kamfanonin da suke aikin samar da zinare 10 mafiya girma a duniya.