1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

M23 ta zargi sojin Kwango da kashe-kashe

August 18, 2014

Tsofuwar kungiyar tawaye ta M23 ta dora alhakin kashe fursunonin yaki a kan dakarun kasar Jamhuriyar Demokradiyar Kwango.

https://p.dw.com/p/1CwUB
Hoto: Reuters

A cikin wata sanarwa da ya karanta, shugaban sashen siyasa na kungiyar ta M23 Bertrand Bisimwa, ya ce cikin kaduwa, da yanayi na cin fuska ne suka samu labarin kisan mutanen da aka kama, wanda jami'an asiri na sojin kasar suka kashesu. Mutanen dai na daga cikin sojin da aka kama a yankin arewacin Kivu a watan Mayu na 2012, da kuma 2013 bisa zargin suna da hannu da 'yan kungiyar M23.

Sai dai tuni gwamnatin kasar ta karyata wannan zargi, inda kakakin gwamnati Lambert Mende, ya ce babu wani mutum da ake kashewa yanzu a wannan kasa, kuma idan ma akwai wanda ake zargi da wani laifi, to ana mikasu ne a hannun shari'a ta soja ko ta farar hulla.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edit6a : Mouhamadou Awal Balarabe