1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Léopold Senghor: Fursuna ya zama shugaban kasa

Robert Adé
October 30, 2020

Léopold Sédar Senghor, wanda ake yi wa kallon dattijo a Afirka, masani ne kuma marubucin wakoki. Bayan zama gidan yari lokacin yakin duniya, ya kasance shugaban kasar Senegal na farko

https://p.dw.com/p/3kgGJ
Portrait Léopold Sédar Senghor

Yaya ake iya takaita tarihin rayuwar Léopold Sédar Senghor?

An haifi shi ne a ranar 9 ga watan Oktoba, 1906, a yankin kudu maso gabashin birnin Dakar na Senegal. Senghor, shi ne jagoran kungiyar fafitikar kare bakar fata ta Négritude, a shekarar 1930. Ya zama shugaban kasar Senegal a cikin watan Satumbar 1960, bayan zama dan jarida daga cikin ayyukan da ya yi. Ya ci gaba da zama shugaban kasa na tsawon shekaru sama da 20. Ya rasu a ranar 20 ga watan Disamabar 2001 a Faransa yana da shekaru 95.

Me ake iya tunawa game da Léopold Sédar Senghor?

Léopold Sédar Senghor, mutum ne mai son zaman lafiya da kawaici, sannan yana da son komai ya tafi daidai a tsarinsa na aiki.  Masani ne da ke da kaunar harsuna. Shi ne bakar fata na farko da ya shiga majalisar marubuta ta harshen Faransanci wato a shekara ta 1984. Sannan dadin-dadawa shi ne shugaban kasar Afirka na farko da ya yi murabus a bisa radin kansa.

African Roots  | Léopold Sédar Senghor

Wadanne kalmomi ne ake alakanta su da Léopold Sédar Senghor?

"Ka fahimta ba don lallai a fahimce ka ba” Daga cikin fitattun kalamansa na hikima, Senghor ke kiran matasan Afirka da su yi kokarin fahimtar duk wani abu da ke da asali da tarihi gami da al'adu, domin karfafa ilimin zuwa ga wani mataki da ya gaza samuwa a zamanin baya.

"Ci gaba mai tafiya da zamani” Wannan kalma ya samo tushe da kuma ma'anar muhimmancin buda hankali don karbo bakon abu mai amfani da kuma mika shi ga na gaba. Manufar hakan shi ne hada wasu abubuwan na bakar fata da wadanda ke da tsatso da turawa domin samun sabuwar tafiya ta bakar fata ko "New Negro” kamar yadda ya fada.

Wadanne abubuwa ne na rashin fahimta da suka shafi rayuwar Senghor's life?

Tsakanin shekarar 1962 zuwa 1968, Léopold Sédar Senghor, ya yi wasu kurakurai a siyasa wadanda suka haddasa wasu kungiyoyin da suka yi masa bore. A 1968 ne masana da dalibai masu alaka da akidar masanin falsafan nan wato 'Karl Max' suka juya masa baya.

Yaya kuma aka karrama Léopold Sédar Senghor ?

Senghor ya karbi kyaututtuka da lambobin yabo da dama. Daga ciki akwai lambar da Faransa ta ba shi matsayin da ake bai wa hazikan sojoji. Akwai ma kwaitar marubuta ta Jamus wato ''German Book Trade'' da kuma wasu digirin girmamawa masu yawa da wasu fitattun jam'i'on duniya suka ba shi. Wurare da cibiyoyi ma yanzu na amsa sunan Léopold Sédar Senghor. Ga ciki akwai filin jirgi da na wasanni na Senegal da Jami'ar  nazarin harshen faransanci a birnin Alexandria na kasar Masar da gidauniyar Léopold Sédar Senghor sai kuma cibiyar Senghor da ke a kasar Portugal.    

Wannan labarin ya samu ne tare da tallafin bayanan kimiyya da kuma na tarihi daga masana irin su; Farfesa Doulaye Konaté da Dakta Lily Mafela, da Farfesa Christopher Ogbogbo. Gidauniyar Gerda Henkel ce ta tallafa wa wannan shiri na Tushen Afirka.