Lura da sauyin yanayi ta tauraron dan Adam | Labarai | DW | 19.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lura da sauyin yanayi ta tauraron dan Adam

Manyan darectocin hukumomin kula da binciken sararin samaniya sun tunatar da mahimmancin tauraron dan Adam kan tafiyar sauyin yanayi.

Masana da suka gudanar da zaman taronsu a birnin Mexiko na kasar Mexiko, na neman ganin an samar da tauraron dan Adam na musamman da zai sa ido kan tafiyar sauyin yanayi, da kuma bin sau da kafa na alkawuran da kasashe za su dauka a yayin babban zaman taro kan sauyin yanayi da zai gudana nan da 'yan watanni a birnin Paris na kasar Faransa. Wannan shi ne karo na farko da masana harkokin sararin samaniya kimanin 30 suka hallara domin tattauna batun na sauyin yanayi bisa wani tsari na Faransa domin tunatar da jama'a irin rawar da tauraron dan Adam zai taka a fannin lura da sauyin yanayi.

Hakan kuma na zuwa kasa da watanni uku kafin babban zaman taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi da zai gudana a watan Disamba a birnin Paris. Masanan sun kara da cewa, duk wasu abubuwa da aka sani kawo yanzu kan sauyin yanayi, an san su ne ta sabili da tauraron dan Adam musmman a fannin hauhawar ruwan teku da kuma dumamar yanayi.