Lumana Afirka: Rikici na kara ta′azzara | Siyasa | DW | 02.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Hama ya haramta taron Dosso na Lumana Afirka

Lumana Afirka: Rikici na kara ta'azzara

Rikicin cikin gida a babbar jam'iyyar adawar Nijar gabanin babban taronta na daukar sabon salo lamarin da ya cilasta shugaban jam’iyyar Hama Amadou ya haramta bangaren jami'yyar da ke son taron a Dosso sabanin a Niamey.

Rikicin cikin gida da babbar jam’iyyar adawa Lumana Afrika ta ke fuskanta ya dauki wani sabon salo tun bayan da shugabanta Hama Amadou da ke gudun hijira ya nuna goyon baya ga matakin wani banagare na kwamitin kolin jam’iyyar Lumana Afrika na cewa babban taron jam’iyyar za a yi shi ne a birnin Yamai, duk kuwa da cewa bangaran shugaban riko Oumarou Noma da ke rike da hukuncin kotu ya ce za a guadanar da baban taron a Birni Dosso. 

A cikin wata hira da kafar yada labarai mai zaman kanta a Niamey Hama Amadou ya bayyaana wadanda suka ce za su gudanar da babban taron Lumana a Dosso sabanin matanin kwamitin koli na Jam’iyyar a Niamey da cewa na shan shayi ne, inda ya ce taron congres daya ne za a yi na Lumana kuma shine wanda za a yi a Yamai.

Kawo yanzu bangaren da ke ikrarin rike jam'iyyar da ya kira taron a Dosso na ci gaba da nazarin matakin da madugun 'yan adawar Hama Amadou ya dauka, inda za su yi sanarwar makomar taron a gaba.

Sai dai madugun 'yan adawar Hama Amadou a karon farko bai tabo batun takararsa ba ta neman shugabancin kasa, kana kuma bai zargi gwamnati ba a hannu cikin barakar cikin gida  da jam'iyyarsa ta Lumana Afirka ke fama da ita ba.

Sauti da bidiyo akan labarin