Likud ta samu nasara a zaben Isra′ila | Siyasa | DW | 17.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Likud ta samu nasara a zaben Isra'ila

Jam'iyyar Likud ta firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta samu nasara a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a jiya Talata.

Jam'iyyar Likud ta firaministan Isra'ila ta samun nasara a zaben da ya gudana a jiya Talata na majalisar dokokin kasar ta Knesset. Sakamakon da ya fita ya nuna cewar Likud din ta samu kujeru 30 daga cikin 120 da ake da ake da su yayin da jam'iyyar Zionist Union ta Isaac Herzog ke biye mata baya da kujeru 24.

Israel Wahlen 2015 Jitzhak Herzog in Jerusalem

Jam'iyyar adawa ta Zionist Union da Isaac Herzog ke jagoranta ta amince da shan kaye.

Wannan nasara da Likud din ta samu za ta iya bata dama ta girka gwamnati a kasar in ta samu nasarar yin kawance da sauran jam'iyyun da su ma suka samu kujeru a majalisar. Tuni ma dai firaministan na Isra'ila ya ce ya fara shirin zantawa da wasu jam'iyyun don kaiwa ga samun abokan kawance har ma ya ce za su samar da gwamanti nan da makonni biyu ko uku.

Israel Wahlen 2015 Likud-Wahlplakate in Tel Aviv

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu ya ce nan da makonni 2 ko 3 zai kafa gwamnati.

Shugaban jam'iyyar Zionist Union Isaac Herzogya amince da shan kaye a zaben, don tuni ma ya fito ya yi wa jam'iyyar Likud din da magoya bayanta murnar samun nasara da ta yi a zaben. Mr. Herzog ya ce ya kira firaminista Netanyahu ta wayar tarho don taya shi murna da kuma yi masa fatan alheri a gwamnatin da zai jagoranta. A baya dai an yi hasashen samun nasara ga jam'iyyar Zionist din da ke adawa sai dai labarin ya sauya bayan fitar sakamakon zaben.