Likitoci sun amince fara farfado da Sharon a yau | Labarai | DW | 09.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Likitoci sun amince fara farfado da Sharon a yau

Likitoci da suke kula da lafiyar firaministan Israila Ariel Sharon,suna shirin farfado da shi sannu a hankali daga alluran suma da sukayi masa nan gaba a yau din nan.

Da zarar ya farfado ne a cewar likitocin zasu tabbatar da yawan dameji da ya samu kwakwalwar firaministan dan shekaru 77 da haihuwa,bayan bugun jini da ya samu da kuma tiyata sau 3 da akayi masa.

Kwararru a fannin aikin likita sunce ko da ma ya farfado,da kyar ne ya koma bakin aikinsa.