Libya ta yi wtsi da bukatar yin afuwa ga jamián lafiya dake fuskantar hukunci a kasar. | Labarai | DW | 18.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libya ta yi wtsi da bukatar yin afuwa ga jamián lafiya dake fuskantar hukunci a kasar.

Ministan harkokin wajen Libya ya yi watsi da kiran da shugaban Amurka George W Bush ya yiwa kasar ta yin afuwa ga wasu jamián lafiya su biyar na kasar Bulgaria wandanda ke fuskantar hukuncin kisa a kasar ta Libya. Jamia´n lafiya su biyar tare da wani likita daya dan kasar Palasdinu an yanke musu hukuncin kisa ne a bara saboda samun su da laifin yiwa wasu kananan yara Allurar kwayar cutar Kanjamau a asibitin Benghazi dake arewacin Libya. Da farko biyu daga cikin jamián lafiyar da kuma Likitan sun amsa tuhumar da aka yi mus kana daga bisani suka ce tilasta musu aka yi saboda azabtar da su da yan sanda suka yi.