Libiya ta kori baƙi | Labarai | DW | 27.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya ta kori baƙi

'Yan ƙasashen Afirka da ke zama a ƙasar Libiya sun fiskanci kora da ga ƙasar, inda aka tura su zuwa Jamhuriyar Nijar

Ƙasar Libiya ta kori kimanin baƙi 'yan ci-rani daga ƙasashen Afirka 500. Kamfanin dillalcin labaran gwamnatin ƙasar ta Libiya, ya ce baƙin an tisa ƙeyarsu zuwa ƙasar Jamhuriyar Nijar ne, a wani matakin rage tuttuɗowar da baƙi yan ci-rani da kuma masu kaifin kishin Islama a ƙasar. Ƙasashen Yamma dai na gudun cewa, ƙasar Libiya za ta kasance wata tunga ga ƙungiyar Alƙa'ida, yayinda a yanzu gwamnati mai rauni ta ke neman kakkaɓe mayaƙa da ke ɗauke da makamai, kana da sauran matasan da aka yi amfani da su a yaƙin kifar da gwamnatin Gaddafi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu