1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Masu safarar bakin haure sun shiga matsi

Salissou Boukari
September 13, 2017

Hukumomin yankin Sabratha da ke a nisan km 70 a yammacin birnin Tripoli a kasar Libiya, sun dauki kwararan matakai na yaki da masu safarar bakin haure zuwa Turai daga yankin ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/2jtSk
Mittelmeer Küste Libyen Rettungsaktion Flüchtlinge
'Yan gudun hijira masu yunkurin zuwa Turai daga LibiyaHoto: Reuters/D. Zammit Lupi

Mataki ya nuna karara da irin ci gaban da aka samu a fannin rage kwararar bakin haure da ke ketarawa zuwa kasar Italiya, inda aka samu mutane 6.500 tun daga tsakiyar watan Yuli kwatankwacin kashi 15 cikin 100 kacal na adadin da aka samu a shekarun 2014 da 2016. A cewar hukumomin na Sabratha, sojojin ruwan Libiya ne tare da hadin gwiwar na Italiya suka tashi tsaye wajen hana ruwa gudu ga ayyukan masu safarar bakin hauren, kuma gwamnatin hadin kan kasar ta libiya na dafawa wajen ganin an samu tafiyar da wannan aiki, sannan suma mazauna yankin da bakin hauren ke tattaruwa a kasar ta libiya, sun yi matsin lamba na ganin an daina tattara musu bakin a yankunan su ko kuma su dauki matakai.