Libiya: Farfado da dangantaka da Jamus | Labarai | DW | 09.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libiya: Farfado da dangantaka da Jamus

Shekaru bakwai bayan kwashe baki dayan jami'an diplomasiyyarta daga Libiya, Jamus ta sake bude ofishin jakadancinta a kasar da ke yankin Arewacin Afirka.

Maas zu Besuch beim libyschen Außenminister Hamid Dbeibades, Premierminister

Firaministan Libiya Hamid Dbeibades da ministan kasashen waje na Jamus Heiko Maas

Ministan harkokin kasashen ketare na Jamus din Heiko Maas ne ya sake bude ofishin jakadancin a Tripoli babban birnin kasar ta Libiya. A cewar Maas Jamus ta dauki wannan matakin ne, ganin irin ci-gaba mai ma'ana da aka samu a Libiyan a shekarar da ta gabata. Libiyan dai ta tsinci kanta cikin yakin basasa, bayan kifar da gawamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar al-Gaddafi a shekara ta 2011. Koda yake an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Libiyan a shekarar da ta gabata ta 2020, tare da kafa gwamnatin rikon kwarya da za ta jagoranci zaben da za a gudanar a kasar a ranar 24 ga watan Disambar wannan shekarar da muke ciki.