Liberia ta ayyana dokar ta ɓaci saboda Ebola | Labarai | DW | 07.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Liberia ta ayyana dokar ta ɓaci saboda Ebola

Shugabar ƙasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta ce gwamnatin ta kafa dokar ta ɓace ne saboda barazanar da cutar take yi ga ruwar al'umma.

A cikin wani jawabi da shugabar ta yi ta ce dole ne gwamnatin ta ɗauki matakai na musammun a kan wannan cuta domin rayuwa. Tun da farko a wani mataki na daƙile yaɗuwar cutar hukumomin Liberia sun rufe makarantun boko tare da ba da hutu ga wasu ma'aiktan wanda aikinsu bai zama dole ba.

Talauci da jahilci da kuma al'ada ta gargajiya, na daga cikin abin da ke janyo cikas a ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na ƙara faɗikar da jama a kan cutar. Yazuwa yanzu sama da mutane 900 suka mutu da cutar ta Ebola a cikin ƙasashen Saliyio da Gini da kuma Liberia.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu