An tsara wannan garabasar ne don masu koyo da suka yi nisa. A mataki na C1 kana iya amfani da harshen Jamusanci a lokacinka na shakatawa, kasuwanci ilimi inda kuma za ka iya fahimtar rubutu masu tsauri ba tare da wahala ba. A mataki na C2 ka fahimci komai kuma za ka iya gabatar da faffadan bayani akan darussa daban daban.