Leipzig ta kare matsayinta na jagorancin teburin Bundesliga | Zamantakewa | DW | 23.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Leipzig ta kare matsayinta na jagorancin teburin Bundesliga

A cikin shirin baya ga sakamakon wasanninn Bundesliga, za kuma ku ji yadda wasannin lig din na Jamus ke daukar hankali a wasu wurare kamar Kadunar Najeriya.

Za mu dauko shirin daga wasannin Bundesliga na Jamus inda a karshen mako kungiyar Hoffenheim ta samu nasara kan Burossia Dortmund da ci 2 da 1, kana FC Cologne ta doke Werder Bremen 1 da nema, yayin da Schalke da Freiburg suka tashi 2 da 2. Ita ma Leipzig ta doke Ausburg 3 da 1. Yayin da Kungiyar Bayern Munich ta doke Wolfsburg 2 da nema.

Kawo yanzu Leipzig ke jarorancin teburin na Bundesliga a Jamus da maki 37 yayin da Mönchengladbach mai maki 35 ke matsayi na biyu. Sannan Bayern Munich tana matsayi na uku da maki 33.

A daidai lokacin da ake shirin tafiya hutun hunturu na gasar Bundesliga ta kasar Jamus Bayan kammala wasan mako na 17 a ranar Asabar din nan da ta gabata, Kungiyar Bundesliga Fans Club Nigeria ta shirya wasan sada zumunci a ranar Lahadi tare da taro magoya bayan Bundesliga kamar yadda ta saba gudanarwa a kowacce karshen shekara.

Zakaran dan wasan kwallon kafar Afirka

Mohamed Salah dan wasan kasar Masar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila ya kama hanyar lashe zama zakaran gwarzon 'yan wasan Afirka a karo na uku a jere. Kamar yadda hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Afirka ke bayarwa duk shekara, hukumar ta nuna cewa kawo yanzu Mohamed Salah ya shiga gaban wadanda suke takara tare a yawan maki.

Fußball Champions League - Gruppe E - KRC Genk v Liverpool

Mohamed Salah da Sadio Sane dukkansu biyu na yi wa Liverpool wasa

Sauran 'yan takarar su ne: Sadio Mane dan kasar Senegal wanda shi ma yake wa kungiyar Liverpool wasa, sai Riyad Mahrez dan kasar Aljeriya da yake wasa a kungiyar Manchester City ita a Ingila. A ranar bakwai ga watan Janairu ake bayyana wanda zai zama gwarzon zakaru na Afirka yayin biki a garin Hurghada na shakatawa da ke kasar Masar.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bude wata cibiyar kula da harkokin wasanni a gundumar Koumassi na kudancin birnin Abidjan da ke kasar Cote d'Ivoire yayin da ya kai ziyara kasar da ke yankin yammacin Afirka a karshen makon da ya gabata. Wata kungiya mai zaman kanta ta gina wannan cibiya domin bunkasa harkokin wasanni tsakanin kasashen Afirka. Mutane da dama sun halarci bikin. Tare da shugaban na Faransa ciki har da Didier Drogba shahararren dan wasan kasar ta Cote d'Ivoire.

Sauti da bidiyo akan labarin