Legas: Tashin farashin kayan gwari ya jefa rayuwar talaka cikin akuba | Zamantakewa | DW | 26.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Legas: Tashin farashin kayan gwari ya jefa rayuwar talaka cikin akuba

A Kudu maso Yammacin Najeriya farashin kayan masarufi na ci gaba da yin tashin gwauron zabi yayin da jama'a ke fama da rashin kudi.

A birnin Legas da ke zama cibiyar hada-hadar kasuwanci a Tarayyar Najeriya, kayan abinci walau na Turawa na masu akwai ko na talakawan kasar yana cikin wani irin hali na fin karfin talaka.

A yayin da wakilinmu na Legas Mansur Bala Bello ya bi wasu kasuwanni a birnin don gane wa idonsa yadda kasuwar ke tafiya, a wani lokacin a kan kara kudi da baka, kamar yadda Alhaji Haruna Mohammed shugaban kasuwar Mile 12 ta kayan Gwari ya yi bayani.

"Ba mu da wata doka amma kasuwa ita ke sayar da kanta. Ba mu da wata dokar da ta ce idan ka zo da kayanka ga yadda za ka sayar."

Kasuwar ta Mile 12 ta fi ko wace kasuwa yawan kayan Gwari a Legas.

Alhaji Mohammed Hunkuyi shi ne sakatare-janar na kasuwar ya yi karin haske kan yadda kayan suke ciki yanzu haka.

"Kamar yadda na nunar albasa da timatir da sauran kayan Gwarin yanzu farashinsu ya daga sosai. Ba wai ya shafi abubuwan da ke faruwa ba ne. Sai dai a ce lokacin kayan da ya kamata a ce ya fito bai riga ya fito ba."

Su ma kayan masarufi na shaguna su ma sun fada wannan tarkon, kamar yadda Malam Zakari Ya'u ya sheda wa wakilinmu na Legas.

"A kullum muka shiga kasuwa muna samun karin farashi. A da Maltina muna sayenta kan Naira 2450.00 amma yanzu ta kai Naira 3000.00 kuma kullum kayan sai tashi suke yi."

Sai dai wani Mr Adeyinka Lasisi ya ce wani farashin babun gaskiya a cikinsa.

"Ka san farashin yana zuwa gaba ya dawo baya. Wasu 'yan kasuwa kuma suna kara farashi babu gaira babu dalili."

 

Sauti da bidiyo akan labarin