Legas: Sana′ar sayar da kayan marmari | NRS-Import | DW | 27.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Legas: Sana'ar sayar da kayan marmari

Wani matshi a birnin Legas da ke kudancin Najeriya ya rungum sana'ar dayar da kayan marmari da ake kira ''Fruit Salad'' don samun rufin asiri.

Shi dai wannan matashi mai suna Umar Abubakar ya shafe sama da shekaru goma a birnin ya na sanasar sayar da Fruit Salad inda kabilu daban-daban ke tururuwa a rumfarsa a yankin Obalende da ke karamar hukumar Etiosa a jihar legas domin sayen kayan marmari.

Duk da cewar Umar dai bai samu yin karatun zamani ba, bai bari jakan ya hana shi nemawa kansa mafita ba kuma a halin da ake ciki a iya cewa wannan sana'a ta sanya shi kere sa'a duba da yadda ya ke samun rufin asiri da kuma tallafin da ya ke bawa wasu matasan wajen samun dan kudin kashewa.

Umar dai ya ce wannan sana'a na taimaka masa wajen bada tallafi ga iyayensa da kuma duk wanda ya bukata. Kwastamomin da ke sayen kayan marmari daga hannun Umar sun yaba da wannan sana'a da ya bijiro da ita kasancewar ba abu ne da aka saba ganin irinsa a Legas ba.