Lebanon: Firaminista Saad Hariri ya sauka daga mukaminsa | Labarai | DW | 15.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lebanon: Firaminista Saad Hariri ya sauka daga mukaminsa

Rahotanni daga kasar Lebanon na cewar firaminista Saad Hariri ya sauka daga mukaminsa bayan da ya kasa kafa gwamnati watanni tara bayan da kasar ta fada cikin rikicin siyasa.

Wannan mataki na zuwa ne jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Michel Aoun wanda ya ce sun kasa samun daidaito a tsakaninsu kan membobin gwamnati.

Sun kwashe tsawon lokaci suna zaman doya da manja, lamarin da ya sa suka kasa cimma matsya da za ta kaisu ga kafa gwamnati.

Firaminista Hariri ya ki amincewa da gyaran da shugaba Awon ya bukata a kan haka ya gwamnace jefar da kwallon mangoro domin ya huta.


Ana ganin wannan mataki zai kara tsunduma kasar ta Lebanon a cikin rudani, baya ga tarin kalubalen da suka shafi tattalin arziki da take fama da su tun tun karshen shekara ta 2019.