Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Wannan ne Kashi na karshe na shirin Tsaka Mai Wuya kuma za mu ji yadda matasan nan wato Ado da Nasir da Hauwa suka shawo kan matsalolinsu.
Shirin da ke bayani a kann rikice-rikicen Afirka da hanyoyin warwaresu mai suna bin sahun kaka da kakanni.
Siyasa da Zamantakewa na da muhinmanci wajen samar da irin sauyin da ake muradi na inganta ci-gabar Al'umma.
Kula da lafiya abu ne da ke da tasiri a rayuwa. Kamar yadda akan ce lafiya jari, kasancewar ita ce uwar jiki, domin sai da ita ake komai. Babu babban arziki da ya fi samun ƙoshin lafiya.
Shirin DW Rediyo na ilimantarwa wa nahiyar Afirka. Waɗanda Suka kunshi wasannin kwaikwayo da bayanai a kan Siyasa da Kiwon lafiya daTattali da Zamantakewa.
Kashi na ɗaya:
Laraba 13:30 UTC, Juma'a 18:30 UTC da Asabar 18:05 UTC
Kashi na biyu:
Juma'a 13:30 UTC, Asabar 13:20 UTC da Litinin 18:40 UTC
Taɓin hankali cuta ce da ake tsangwama a yawancin al’ummomin Afirka. Akan mayar da masu fama da ita saniyar ware.
Duniya na ci-gaba da fuskantar sauyin yanayi. Wane tanadi muke da shi na kalubalantar wannan juyi da duniya take ciki? Yana da muhimmanci mu samu hanyoyin bunkasa tattalin arziki domin dogaro da kai.
Zaman lafiya da juna shi ne ginshiƙin ci-gaban ko wace Al'umma. Ta haka ne za'a daraja wa juna tare da samar da haɗin kan aiki tare, domin samar da ingantacciyar ci-gaba da ake muradi.
Muna farin ciki tare da marhabin da ra'ayoyin masu sauraro, dangane da shirinmu na Ji Ka Karu. Kuna iya aiko mana ta adireshinmu na E-mail ko kuma ta wasika.
Shirin Ji ka karu sai daɗa bunƙasa yake yi! An samu ƙarin ƙwararru masu sha'awar shirin da suka haɗe da mu domin ƙara kyautata shirin don jin daɗin masu sauraro. Ga dai fuskokin sabbin masu taimaka wa shirin Ji Ka Ƙaru