Lawyoyi a Niger sun fara wani yajin aiki | Labarai | DW | 11.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lawyoyi a Niger sun fara wani yajin aiki

A yau Litinin ne lawyoyi a Jamhuriyar Nijar suka shiga wani yajin aiki biyo bayan zaman majalisar lawyoyin ta kasa da ta yi don nuna fushunta ga gwamnati.

Majalisar lawyoyin ta dauki wannan matakin ne don nuna bakin cikin kan kame-kamen da ake yi ma wasu 'yan siyasar adawar kasar da ake tuhumar da hannu a yunkurin kifar da mulkin da bai ci nasara ba.

Shugaban majalisar lawyoyin Samna Soumana Daouda ya ce ya na da kyau a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu ba wai a ci gaba da tsaresu ba.

Yanzu haka dai al'amura na ci gaba da zafafa a yayin da ake tsare da Hama Amadou dan takarar shugabancin kasar da katun kundun tsarin mulki ta amince da takararsa.