Lavrov: Za mu shiga tsakanin rikicin Katar | Labarai | DW | 10.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lavrov: Za mu shiga tsakanin rikicin Katar

Ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ya ce kasar sa Rasha a shirye take ta shiga tsakani a rikicin da ya hada Katar da makwabtan ta na yankin Gulf.

Kasar Rasha ta yi kira da a tattauna tsakanin Katar da makwabtant a na yankin Gulf domin warware rikicin da ke tsakanin su. Ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ya nuna wannan bukata a birnin Moscow lokacin da ya gana da takwaran aikin sa na Katar Sheikh Mohamed ben Abderrahmane Al-Thani. Sannan ya kara da cewar Rasha a shirye take wajen taimakawa don warware rikicin.

Kasashen Saudiyya da Bahrain, da Masar, da Hadeddiyar Daular Larabwa sun katse huldar dipolomasiyya da kasar Katar bisa zargin ta da tallafa wa ayyukan ta'addanci. Sannan Saudi Arabiyya ta rufe iyakokinta na ruwa da sama da kasa, lamarin da ya katse hanyoyin shigo da kashi 40% na abincin da Katar ke bukata.