1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ivory Coast: Komawar Laurent Gbagbo gida

Abdul-raheem Hassan AMA
June 17, 2021

Tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ya koma gida bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta wanke shi daga zargin laifukan cin zarafi a rikicin bayan zaben 2010.

https://p.dw.com/p/3v6Ak
Niederlande Den Haag I Prozess Elfenbeinküste am Internationalen Gerichtshof
Hoto: Jerry Lampen/AP/picture alliance

A shekarar 2010, an gudanar zaben shugaban kasa a Cote d'ivoire, bayan jan kafa game da batun dage zaben har sau shida tun a 2005. Kotun tsarin mulki ta tabbatar da nasarar Laurent Gbagbo a matsayin zababben shugaban kasa, amma hukumar zaben ta yi watsi da ikirarin tare da ayyana Alassane Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben, ita ma Majalisar Dinkin Duniya  ta goyi bayan Alassane Outtara.Sai dai duk da haka Shugaba Gbagbo a lokacin ya ki ba da kai.

Karin Bayani: Gbagbo zai iya komawa gida - Ouattara

A shekarar 2011, bayan tashin tashina na tsawon watanni hudu da gazawar yunkurin sasanta juna, dakarun da ke biyayya ga Ouattara da taimakon 'yan tawayen da suka dauki makamai a yankin arewacin kasar sun sami iko da mafi yawa na kasar Ivory Coast. Faransa da Majalisar Dinkin Duniya sun jibge sojojinsu a babban birnin kasar Abidjan don hana amfani da manyan makamai a rikicin. Amma bayan kwanaki 10 da aka shafe ana barin wuta a birnin, Laurent Gbagbo ya shiga hannun dakarun sojan da ke goyon bayan Alassane Ouattara, sama da mutane 3,000 sun mutu a rikicin. A watan Mayu 2011, an rantsar da Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa, an kuma sake zabansa a 2015, kafin ya yi tazarce a shekarar 2020.