Lauran Bagbo ya sa hannu a kan dokar haɗewar rundunar tawaye da dakarun gwamnati | Labarai | DW | 17.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lauran Bagbo ya sa hannu a kan dokar haɗewar rundunar tawaye da dakarun gwamnati

Shugaban ƙasar Cote d´Ivoire Lauran Bagbo ya sa hannu a kann dokar haɗe rundunar yan tawayen FN, da dakarun gwamnati.

Bagbo ya ɗauki wanann doka, a sakamakon yarjejeniyar sulhu, da ɓangarorin 2 su ka cimma, a birnin Ouagadougou na Bourkina Faso.

Kazalika, shugaban ƙasar, ya girka wani komiti na mussamman, wanda zai gudanar da saban tsari, ga rundunar tsaro ta ƙasa, da zata ƙunshi dakarun rundunonin guda 2.

A yammacin jiya,an gana tsakanin shugaban baradan tawaye, Jannar Sumaila Bakayoko, da kuma na rundunar gwamnati, Jannar Philipe Mangu.

Sannan sun shirya wata ganawa yau, a birnin Bouake, da zumar kai ga mattakan gaggauta girka rundunar haɗin gwiwar.