Larabawa sun gaza tallafawa Palasdinu da kudi
February 21, 2006Mideast
Ministocin harkokin waje na kasashen larabawa sun gaza cimma yarjejeniya a dangane da bawa Palasdinu tallafi ,akarkashin gwamnatin Hamasa dangane da sabanin raayi kann tallafi daga kowace kasa.Kasashe uku daga cikin kungiyar ne suka bada tallafin kudi wa palasdinawan,inji jamian Algeria a taron wakilan kungiyar daya gudana zuwa tsakar daren jiya a birnin Algiers.
Sakataren kungiyar kasashen larabawa Amr Moussa da ministan harkokin wajen Algeria Abdelaziz Belkhadem sun kaddamar da asusun neman tallafi daga kasasgen ,domin agazawa sabuwar gwamnatin Palasdinu.To sai dai a taron da suka gudanar da manema labarai,jamian sunki bayyana kasashen da suka bayyana adfawa da wannan yunkuri.Amr Moussa yace dakatar da tallafi da kasar Amurka da Kungiyar gamayyar Turai sukayi barazana,zai haifarwa palasdinawan matsaloli.A dangane da hakane ya jaddadawa kasashen larabawan cewa,wannan tallafin zasu bayar ne wa jamaar palasdinu ,amma bawa Hamas ba.