Larabawa na neman warware rikicin Syriya | Labarai | DW | 25.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Larabawa na neman warware rikicin Syriya

Shugabannin kasashen Larabawa na gudanar da taronsu na shekara-shekara a kasar Koweit, inda a wannan karon za su dukufa kan rikicin kasar Siriya don neman mafita.

A wannan Talatar ce (25.03.2014) ake soma taron Shugabannin kasashen Larabawa na shekara-shekara a kasar Koweit, inda mahalarta taron suka amince da mayar da duk wani sabanin dake tsakaninsu gefe guda, domin nemo mafita ga wannan rikici na kasar Siriya.

Shugaban hadin gwiwar 'yan adawar kasar Siriya Ahmad al-Jarba, zai yi wani jawabi bayan bude wannan taro, duk kuwa da cewa ba zai iya zama a kan kujerar kasar siriya ba, ganin cewa hadin gwiwar yan adawar basu cika sharuddan yin hakan ba, sakamakon dakatar da kasar daga cikin wannan kungiya a shekarar 2011.

A nashi bangare mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin duniya kan rikin kasar Siriya Lakhdar Brahimi, za iyi nashi jawabi a gaban shugabanni kasashen 22 membobin wannan kungiya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe