Lamura sun fara daidaita a Kanada | Labarai | DW | 23.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lamura sun fara daidaita a Kanada

Rahotanni daga Kanada na cewar lamura sun fara daidaita bayan wasu jerin harbe-harbe da wani dan bindiga ya yi a ginin majalisar dokokin kasar.

Masu aiko da rahotanni suka ce mutanen da ke aiki a majalisar dokokin kasar sun fara zuwa wajen aiki ko da dai an tsaurara matakan tsaron a wajen. Kowane lokaci daga yanzu ne ma ake sa ran majalisar za ta fara zamanta don gudanar da harkokinta kamar yadda ta saba.

Yayin zaman majalisar dai ana sa ran firaminstan kasar Stephen Harper zai gudanar da jawabi gaban 'yan majalisar, yayin da a hannu guda 'yan majalisar za su hadu a kusa da ginin majalisar dokokin kasar don girmama sojan da ka harbe a jiya yayin da ake musayar wuta da dan bindigar da ya kashe shi wanda shi ma ya ya rasu daga baya.

Gwamnatin ta Kanada dai ta ce hare-haren da aka kai ba za su sanyaya mata gwiwa wajen gudanar da aiyyukanta ba kuma za ta cigaba da yin bakin kokarinta wajen ganin ta yaki ta'addanci a kasar baki daya.