Lafiya jari: Mata masu yoyo fitsari na wahala | Zamantakewa | DW | 15.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Lafiya jari: Mata masu yoyo fitsari na wahala

Mata masu fama da ciwon yoyon futsari a Najeriya na fuskantar kyama da tsangoma a tsakanin al'umma wannan shi ne batun da shirin lafiya jari ya duba.

Cutar yoyon fitsari wata lalura ce da kan auku ga mata mussaman masu kananan shekaru, ko da yake masana kiwon lafiya sun bayyana cewar mata kan sami wannan lalura ta yoyon fitsari ko da kuwa sun jima a gidan aure. A sashen da ake kula da mata masu fama da wannan lalura ta yoyon fitsarin da ke a Jos da kwai mata da dama da suka fito daga ciki da wajen Najeriya wadanda ke kwance suna samun kulawar likitoci, wata mace mai suna Suzana Kefas daga jihar Taraba ta ce an yi mata tiyata har sau biyar kafin ta soma ganin alamun sauki.

Sauti da bidiyo akan labarin