Laberiya: Ba da ilimi ga yara da ke gararamba kan titi | Himma dai Matasa | DW | 09.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Laberiya: Ba da ilimi ga yara da ke gararamba kan titi

Mawaki Victor Brown ya dukufa wajen sama wa yara a kasar Laberiya tarbiya ta gari. Yanzu haka yana tallafa musu wajen neman ilimi.

A lokacin da yakin basasa ya barke a kasar Laberiya a shekara ta 1989 akalla mutane dubu 10 ne suka rasa rayukansu, lamarin da ya sa yara rasa samun ilimi. Amma yanzu wani mawaki Victor Brown ya dauki gabarar yaki da makomar tarbiyar yaran kasar. Yawancin yara a kasar sun samu matsaloli matika bama na yakin kadai ba har ma da talauci da cin hanci da tashe-tashen hankula, kuma ana zarginsu da yawan aikata laifuka a babban birnin kasar wato Monroviya.

Shahararran mawakin kasar Victor Brown ya sha alwashin kula da tarbiyar yaran a birnin Monroviya. Shi dai Victor Brown wanda aka fi sani da "T1" yakan hau wani gini da ba a kammala ba ya rika yin rawa gami da waka da ya koya daga mai kidansa Isaac Peter.

Victor Brown na shirye- shiryen fara karatu a babban birnin Laberiya, yana mai cewa:

"A ko da yaushe ina kokarin ganin na shiga makaranta da kuma samun makarantar da zan hadu da wanda ya koya mun waka, kuma sai gashi na yi sa'a na hadu da shi. Ya gaya mun kalmomin da suka karfafa mun guiwa. Ya ce zan iya taimaka maka domin ka fara karatu, kuma hakan ya sa ya kara mun kwarin guiwar sana'ata ta rawa da waka, kuma ya ce zan iya zuwa makaranta in yi rawa akalla zan iya jan hankalin abokaina wadanda ba su da ilimi ta yadda za su samu shiga makarantu."

Damar samun ilimi ga yara masu gararamba

Isaac Peter na daya daga cikin wadanda suka rasa matsugunni sakamakon yakin kasar ta Laberiya kuma ya kwashe yarintarsa a kan titi. Amma yanzu ya gina makaranta dan samar da dama ga yara masu gararamba kan tituna su samu su shiga makarantar domin samun ilmi.

AoM Ausbildung Straßenkinder in Liberia

Darasi ga yara marasa galihu a Laberiya

Peter ya ce ya cigaba da fadi tashin ganin makarantar ba ta dirkushe ba tun shekara ta 2003.

"Gararamba a bakin tituna a lokacin ya bani damar shirya kyakkyawar makoma. Tanadin kyakkyawar makoma wani abu ne mai zaman kansa amma hakan ya taimaka mun yin tasiri ga rayuwar sauran mutane."

Wannan dai ba ita kadai ba ce kwarewar da ta karfafa wa Peter guiwar taimaka wa yara a kasar ba. Shigar dansa Sirius ayyukan da ba su dace ba na daga cikin karin dalilansa, kuma rasa dansa Sirius na daga cikin bala'in da ya kara karfafa masa guiwa. Sirius dai ya saba zama tare da Peter kafin ya fara sata. Lokacin da ya kai wa mahaifinsa hari sau daya bayan tashi daga makaranta. Peter sai ya yanke shawarar canza masa wurin zama zuwa wani yanki na daban, yayin da ya kara da cewa.

"Na ga ya zama wajibi gare ni, in canza masa mazauni zuwa wani wuri wanda ka iya canza masa rayuwarsa da ma ta sauran mutane."

Karfafa guiwar manyan gobe don samun kyakkyawar makoma

Peter ya cigaba da karfafa wa yara guiwa wajen samun kyakkyawar makoma musamman ta yadda za su yi karatu su zama masu dogara da kansu ta hanyar koyan sana'o'i daban-daban.

"Idan kuna bukatar koyan kanikanci za mu iya kokarin hakan, ko sana'ar kafinta da ma sana'ar gyaran famfunan ruwa, duk za mu iya yi maku kokarin hakan ku dai bari mu gani."

Shi kuma Victor Brown dai ya cigaba da gudanar da harkokinsa na rawa a birnin Monroviya yayin da yakan tara yara yana nuna masu muhimmancin ilimi ga rayuwarsu domin su zamo masu amfani a cikin al'ummar kasar ta Laberiya.

Sauti da bidiyo akan labarin