1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni

Suleiman Babayo
January 30, 2018

Sakamakon gasar tennis na Ostireliya da aka kammala, gami da sakamakon wasannin lig na wasu kasashen Turai, da wasu fannonin na wasanni.

https://p.dw.com/p/2rlH1
Tennis | Roger Federer gewinnt Australian Open
Hoto: Reuters/I. Kato

A karshen mako aka kawo karshen gasar kwallon Tennis na Ostireliya Open, inda Roger Federer ta samu nasara a bangaren maza bayan doke Marin Cilic. Wannan ke zama karo na 20 da Federer dan kasar Switzerland mai shekaru 36 da haihuwa ke lashe manyan wasannin duniya na tennis.

Yayin da Caroline Wozniacki ta samu nasara a bangaren mata tare da komawa kan tebur a matsayi na farko na kwanayen kwallon tennis na mata na duniya.

Tennis Australian Open 2018 Caroline Wozniacki
Hoto: Reuters/I. Kato

 

A wasannin lig na Bundesliga na Jamus da aka kara a karshen mako, inda Borussia Dortmund ta tashi 2 da 2 da kungiyar Freiburg, sannan FC Kolon ta tashi 1 da 1 da kunguyar Augsburg, kana Leverkussen ta doke Mainz 2 da 0. Ita kuwa Bayern Munich ta kacaca wa kungiyar Hoffenheim 5 da 2.

Fußball: 1. Bundesliga 20. Spieltag Hannover 96 - VfL Wolfsburg
Hoto: Imago/Nordphoto

Har yanzu Bayern Munich ke jagorancin teburin na Bundesliga da maki 50, yayin da Leverkussen take matsayi na biyu da maki 34, ita ma Schalke da maki 34 a matsayi na hudu.

A kasar Spain:

Valencia 1, Madrid 4

 Malaga 0, Girona 0

 Villarreal 4, Sociedad 2

 Sunday's Matches

 Leganes 3, Espanyol 2

 Atletico 3, Las Palmas 0

 Sevilla 1, Getafe 1

 Barcelona 2, Alaves 1

	Spanien Real Madrid vs FC Barcelona
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Seco

Har yanzu Barcelona ke jagorancin teburin na La Liga a Spain.

Yayin da ake shirye-shirye gasar neman cin kofin kwallon kafa na duniya da Rasha za ta dauki cikin wannan shekara ta 2018, wanda kasashen Afirka biyar suke cikin wadanda za su fafata. Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashe.

Dan kasar Jamus, Gernot Rohr mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ya ce suna sane da kalubalen.

"Runkunin da muke ciki mawuyaci ne, na kungiyoyin da suka hada da Argentina sun lashe kofin sau biyu, akwai Iceland da Croatia wadda take gaba-gaba a Turai. Amma ina da yakinin za mu iya samun nasara kan kungiyoyin da ake gani sun wuce mu, saboda muna da 'yan wasan masu matsakaicin shekaru. Kuma ana tsammani za mu yi gaba har zuwa karshen wasan."

Fussball African Cup 2017 - Nigeria - Nationaltrainer Gernot Rohr
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Sannan Gernot Rohr duk ya yana horas da 'yan wasan Najeriya amma ya yaba da sauran kasashe hudu wadanda za su wakilci Afirka lokacin gasar na neman cin kofin kwallon kafa na duniya nan gaba cikin wannan shekara ta 2018 a kasar Rusha.