Labarin Wasanni | Zamantakewa | DW | 03.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin Wasanni

Wasannin Lig-lig na wasu kasashen Turai, da kasuwar cinikin 'yan wasa da kuma wasannin cin takobin kokowar gargajiya a Jamhuriyar Nijar.

Wasannin kwallon kafar kasar Ingila na Premier Ligue  inda a karshen mako aka buga wasannin mako na 21 inda wasan da ya fi daukar hankali shi ne cin kacar da  kungiyar Chelsea ta yi wa  Stoke City ta ci 5-0, a yayin da Liverpool ta doke Leicester da ci biyu da daya. Dan wasan gaba na kungiyar ta liverpool dan kasar Masar da taurarinsa ke haskawa a bana wata Mohamed Salah ne ya ci wa kungiyar tasa kwallayen guda biyu.

Har yanzu dai kungiyar Manchester City ce ke kan saman tebirin na Premier Lig, kungiyar Chelsea na a matsayin ta biyu da maki 45 a yayin da Manchester united ta koma a matsayin ta uku da maki 44.

Har yanzu muna kan batun na Premier Lig inda a karshen mako jaridar Daily Mail ta wallafa sunayen 'yan wasan Premier League guda 40 da suka fi albashi mai tsoka.

Dan wasan tsakiya na Kungiyar Manchester United dan kasar faransa Paul Pogba ne dai ke a sahun gaba inda yake daukar albashin Euro dubu 290 a kowane mako, Romelu Lukaka dan kasar belgiyam da shi ma ke buga wa kungiyar Manchester United na bi masa da albashin Euro dubu 250 a ko wane mako , dan kasar Ajentina Sergio Aguero da Yaya Toure dan kasar Cote d'Ivoire da ke bugawa Manchester City da kuma Zlatan Ibrahimovic na Manchester United na a matsayin na uku da albashin euro dubu  220 a mako.

Yanzu kuma sai kasuwar cinikin 'yan wasa inda yanzu haka wasu manyan 'yan kwallon kafa na duniya suka bayyana sha'awar ficewa daga cikin kungiyoin da suke taka leda. Daga cikin 'yan wasan da ke da wannan aniya akwai Cristiano Ronaldo wanda jaridar Daily karshen mako ta ruwaito cewa ya shaida wa kungiyarsa ta Real Madrid bukatarsa ta sayar da shi a karshen kakar wasannin shekarar bana a farashin euro dubu 100. Jaridun Birtaniya sun bayyana cewa a halin yanzu akwai rashin jituwa ne tsakanin dan wasan da shugaban Kungiyar ta rea Madrid Florentino Perez a game da batu albashi da dan wasan ke son a kara masa ta yadda zai kan wanda Leonel Messi da kuma Neymar suke samu a kungiyoyinsu na Barcelona da kuma PSG.

Wannan taurarin dan wasan da ya bayyana sha'awar ficewa daga Kungiyarsa shi ne Eden Hazzard wanda ke buga wa Chelsea wanda jaridar Telegraph ta ruwato cewa ya ki amincewa da tayin tsawaita kontarjinsa da Kungiyarsa ta Chelsea ta yi masa., batun da hatta mahaifinsa ya tabbatar. Jaridar ta bayyana cewa dan wasan na son canza sheka ne zuwa kungiyar Real Madrid kungiyar da ya jima yana bayyana sha'awar taka mata leda. Sai dai kuma jaridar ta ce kungiyar Chelsea na shirin sake gabatar mashi da wani sabon kontarji mafi tsoka domin shawo kansa kan ya ci tuwan fashi daga bukatar tasa ta komawa Real Madrid.

Dan wasan kasar Ajantina da ke buga wa kungiyar Juventus wato Pablo Dybala shi ma a cewar jaridun Birtaniya ya bayyana bukatar ficewa daga kungiyarsa a sakamakon gajiya da ya fara yi da zaman benci. Dan wasan wanda wasu ke yi masa kallon sabon leonel Messi da kuma ya kai kungiyar tasa a wasan karshe na ci kofin zakarun turai a kakar wasannin bara na fuskantar kalubale ne a kakar wasannin Seria A na bana inda mai horas da kungiyar ta juventus ya ke aje shi a saman benci a wasanni da dama. Akan haka ne ya bayyana bukatar komawa Kungiyar PSG. Sai dai a wasan da Kungiyarsa ta buga a ranar Asabar Pablo Dybala ya sake haskawa inda ya ci wa Kungiyarsa kwallaye biyu daga cikin uku kungiyar tasa ta zira a karawar uku da daya da ta yi da kungiyar Hella Verone.

Yanzu kuma sai wasannin cin takobin kokowar gargajiya karo na 39 da ke gudana a yanzu haka a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar inda daga cikin 'yan kokowa 80 sama da 60 suka sha kasa ya zuwa yanzu.