1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Dortmund ta kusa kamo Bayern

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
November 22, 2021

Manchester United ta Ingila ta sanar da lokacin da za ta nada sabon mai horas da 'yan wasanta, bayan da ta raba gari da Ole Gunnar Solskjær sakamakon baras da wasanni da dama da ya yi.

https://p.dw.com/p/43LCF
UEFA Champions League | Atalanta 2-2 Manchester United
An kori mai horas da Manchester United, sakamakon rashin tabuka abin a zo a ganiHoto: Luca Bruno/AP Photo/picture alliance

Kwanaki biyu bayan raba gari da mai horaswarta, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kayyade lokacin da za ta sanar da wanda zai maye gurbin Ole Gunnar Solskjær wanda ya kasa tabuka abin kirki a wasannin Premier League na baya-bayannan. Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta, Man U ta ce sai nan da karshen kakar wasanni ne za ta sanar da sunan sabon manajanta. Tuni ma dai ta nada Michael Carrick tsohon dan wasanta na tsakiya kuma daya daga cikin mataimakan masu horaswa na kungiyar, a matsayin mai bai wa 'yan wasanta horo na wucin gadi. Ita dai Manchester United ta sallami Ole Gunnar a Asabar din karshen mako, sakamakon shan kashi tamkar kurar roko da kungiyar da yake horaswa ta yi da kwallaye hudu da daya a hannun Watford. Dama dai cikin makonnin da suka gabata, abokan gabatarta Liverpool da Manchester City sun bi Manchester United din har gida kuma suka gasa mata aya a hannu, lamarin da ya fusata dimbin magoya bayan da take da su a fadin duniya.

UK Premierleague | Manchester United vs Liverpool
Manchester United ba ta ji da dadi ba a karawarta da LeverpoolHoto: Oli Scarff/AFP/Getty Images

Shekaru uku mai horas da 'yan wasan Ole Gunnar dan Norway ya shafe yana jagorancin kungiyar Manchester United, ba tare da kofi ko daya ba. Sai dai an fara rade-radin cewa United ta fara tattaunawa da Zinedine Zidane na Faransa, domin ya zama sabon mai horas da 'yan wasanta saboda rawar da ya taka a Real Madrid. Amma jaridun Birtaniya sun ambato sunayen Brendan Rogers da Erik ten Hag da Luis Enrique da kuma Mauricio Pochettino a matsayin na sahun gaba a wadanda United din za ta iya dora fatanta kansu.

Yanzu kuma sai mu je kasar Faransa, inda alkali ya katse karawar da aka yi tsakanin Olympique Lyonnais da Olympique Marseille bayan da aka jefe dan wasa Dimitri Payet da kwalbar ruwa a tsakar ka. Wannan dai ba shi ne karon farko da aka katse wasan Ligue 1 a kakar wasa ta bana a Faransa ba, ko cikin watan Agustan ma sai da alkalin wasa ya dakatar da wasa tsakanin Montpellier da Marseille bayan da wani dan wasan OM ya ji rauni a kai sakamakon jifansa da aka yi. Hakazalika makonni kalilan bayan wannan ma an katse wasa tsakanin Nice da Marseille na tsawon mintuna, bayan mamaye filin wasan da fada tsakanin 'yan wasa da magoya baya. A takaice dai sau shida ne aka samu hatsaniya tun farkon kakar wasannin la Ligue na Faransa. Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa za ta yi zama na musamman a wanan Litinin din, domin yanke shawara kan matakan ladabtarwa da za ta dauka. Wannan ba ya rasa nasaba da zargin junansu da zama umul'aba'isin rashin ci gaba da karawar da jami'an Lig da kuma na kungiyoyin kwallon kafa ke yi.

Fußball Bundesliga FC Augsburg v Bayern München
FC Augsburg ta lallasa kungiyar Bayern MünchenHoto: ANDREAS GEBERT/REUTERS

A nan Jamus kuwa mako na 12 na Bundesliga ya zo da wani abin mamaki inda dan-tsako ya kada giwa, ma'ana kungiyar Augsburgb da ke zama 'yar baya ga dangi ta doke Yaya-Babba Bayern Munich da ci 2 da 1. Wannan dai shi ne  karon farko da Bayern Munich ta sha kashi a gasar Bundesliga a bana. Amma kuma abin takaicin shi ne, Augsburg ta kasance a matsayi na 16 a teburin Bundesliga sannan kuma tana tsaka da fama da rikici na cikin gida. Sai dai tsofuwar kura ta Bayern Munich Thomas Müller ya ce su saka sayi ruwan dafa kansu. To da ma dai Hausawa kan ce faduwar wani tashin wani domin kuwa baras da wasan da Bayern Munich din ta yi, ya bai wa Yaya-karama Borussia Dortmund damar cike makin da ke tsakaninsu, inda a yanzu Bayern ke saman teburi da maki 28 yayin da Dortmun ke biye mata baya da maki 27. Ita dai Borussia Dortmund ta lallasa Stuttgart da ci biyu da daya a gida, kuma godiya ta tabbata ga kyaftain dinta Marco Reus da ya ci wa kungiyarsa kwallo na biyu.
Sai dai kuma sabanin Dortmund, ta ware wa Freiburg wacce ta fadi a gida a hannun Eintracht Frankfurt da ta doke ta da ci biyu da nema duk da mamaye wasan da ta yi. Duk ma da cewa Freiburg ta ci gaba da kasancewa a matsayi na uku, amma ratar maki bakwai ne ke raba ta da saman teburi. Ita kuwa Bayer Leverkusen wacce ke a matsayi na hudu, ta lallasa Bochum da ci daya mai ban haushi. Sai dai karawar 'yan gida daya wato darby da aka yi a bangaren Berlin, Union Berlin ta samu nasara a kan abokan hamayyarta Hertha Berlin da ci biyu da nema, sakamakon bajintar da dan Najeriya Taiwo Awoniyi ya nuna, inda ya ci kwallonsa ta takwas sakamakon abin da ya kira aiki tukura da suka gudanar. A yanzu dai Union Berlin na a matsayi na biyar kuma tana da yawan maki daidai da Wolfsburg da ke a matsayi na ta shida. Ita dai Wolfsburg da yi nasarar tashi canjaras biyu da biyu, a wasa tsakaninta da Bielefeld sakamakon farke kwallon na biyu da dan asalin Najeriya Lukas Nmecha ya yi. Wasan da aka fi cin kwallo shi ne wanda Borussia Mönchengladbach ta dandaka Guerther Fürth da ci hudu da nema. Yayin da Hoffenheim ta doke Leipzig da ci biyu da nema su kuwa Mainz da Cologne suka tashi kunnen doki daya da daya.

Bundesliga - TSG 1899 Hoffenheim v RB Leipzig
RB Leipzig ba ta ji da dadi ba a hannun TSG 1899 HoffenheimHoto: Kai Pfaffenbach/REUTERS
Bundesliga - Borussia Dortmund v VfB Stuttgart
Borussia Dortmund ta kusa kamo Bayern Munich a makiHoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

A Jamhuriyar Nijar wani zakaran damben zamani na Boxing da ya tafi ritaya ya dukufa wajen koyar da matasa saboda ceto su daga hali na shaye-shaye da watangariri a kan titi da suka samu kansu a ciki dabarun kare kai a kyauta, domin ba su wata dama ta gina wa kansu makoma. Shi dai Abdoul-aziz ya danganta wannan aiki nasa da gudunmawa wajen ceto matasa musamman masu shaye-shaye da almajirai da ma wadanda suka shiga gantali bayan sun yi watsi da makaranta, domin samar musu da mafita. Kuma tuni daya daga cikin yara da suka samu horo daga Abdoul-aziz ya yi nasarar samun kambu har hudu a cikin shekara guda a damben kasa da kasa.

China  Peng Shuai Australian Open
Peng Shuai ta shaki iskar 'yanciHoto: Adnan Abidi/Reuters

Yanzu kuma sai fagen tennis, inda Alexander Zverev na Jamus ya lashe gasar Masters ta Turin bayan da ya doke Daniil Medvedev wanda ke kare kambun da ci shida da hudu da kuma shida da hudu. Zakaran gasar Olympics a Tokyo, Alexander Zverev ya kammala wannan shekara da nasara 59, lamarin da ke zama mafi kyawun sakamako ga dan wasan Tennis a 2021. A daya bangaren kuma 'yar wasan tennis ta Chaina PPeng Shuai da ta bace sama da makonni biyu, ta sake bayyana a jiya Lahadi. Shugaban Kwamitin Olympil na Duniya Thomas Bach ne ya bayar da wannan sanarwa, bayan da ya yi magana da ita da kafar bidyo. Sai dai  Bach ya ce yayin tattaunawar, Peng Shuai ta bayyana cewa tana cikin koshin lafiya a gidanta da ke birnin Beijing, amma tana son a mutunta sirrinta. Wannan ne karo na farko da aka yi musayar bayanai kai tsaye tsakanin 'yar wasan da jami'an da ke wajen kasar Sin, tun bayan labarin da ya karade dandalin sada zumunta cewa tsohuwar lamba dayan ta tennis  a duniya ta zargi wani babban tsohon jami'in gwamnatin kasar Chaina Zhang Gaoli da yin amfani da karfi wajen yin lalata da ita.