1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bitar gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta 2019

Suleiman Babayo GAT
July 22, 2019

Bayan kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka karo na 32 a kasar Masar wacce kasar Aljeriya ta lashe, mun yi bitar muhimman abubuwan da suka wakana a gasar da suka hada da soma amfani da taimakon alkalancin bidiyo.

https://p.dw.com/p/3MXJd

Kasar Aljeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka karo na 32 da ta wakana a kasar Masar bayan da ta doke Senegal da ci daya da babu. Najeriya ta zamo ta uku a gasar bayan da ta doke Tunusiya da ci daya da babu a wasan neman matsayi. A karon farko kuma an yi amfani da taimakon alkalancin bidiyo a gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka.