1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 30.11.2020

Suleiman Babayo AMA
November 30, 2020

Shirin ya duba ci gaba da alhinin rasuwar dan wasan kwallon kafa, Papa Bouba Diop, na kasar Senegal alhini gami da jana'izar shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Diego Maradona.

https://p.dw.com/p/3m0FG
Senegal 1 Frankreich 0 (2002 WM)
Pape Bouba Diop dan wasan kwallon kafa na Senegal Hoto: imago/Camera 4

Ana ci gaba da alhinin rasuwar dan wasan kwallon kafa, Papa Bouba Diop, na kasar Senegal wanda ya taka rawar gani da jefa daya daga cikin kwallonyen da suka sauya tarihi a wasan cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara ta 2002, in ya ci kwallo daya tila da Senegal ta doke Faransa lokacin bude wannan gasa, kuma lokacin da Faransa take rike da kofin na duniya bayan lashe gasar shekarar 1998. Papa Bouba Diop ya bar duniya yana da shekaru 42 da haihuwa kamar yadda hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Senegal ta bayyana mutuwar. Shi dai Maraigayi Diop da ya zama gwarzo a kasarsa ta Senegal ya yi wasa a kungiyoyin Lens, Fulham, West Ham United and Birmingham City.

Jimamin mutuwar Diego Maradona

Bildergalerie | Diego Maradona: Sportwelt trauert um argentische Fußball-Legende
Alhinin rasuwar Diego Maradona Hoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

A makon jiya aka yi alhini gami da jana'izar shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Diego Maradona, kuma 'yan sanda suka ci gaba da cincciken likitocin da suka kula da tsawon dan wasan na Ajantina, ko sun yi sakaci. Marigayi Maradona wanda ya bar duniya yana da shekaru 60 da haihuwa, ya kasance daya daga cikin 'yan wasan kwallon kafa mafiya tasiori a tarihin kwallon kafa na duniya, kuma yana cikin wdaanda suka fito da sunan Ajantina idon duniya sakamakaon shahara a kwallon kafa. Shi kansa Ali Bin Nasser tsohon alkakin 'yan wanda na farko daga kasar Tuniya da ya yi alkacin wasan kwallon kafa na duniya, wanda shi ne alkali yayin wasan tsakanin Ingila da Ajantina lokacin da Marigayi Diego Maradona ya kara tarihi na farko wajen jena kwallon da hunnu amma ya nuna kamar da ka yi sai kwallon na biyu wanda ya dauko tun kafin tsakiyar fili ya shiga tsakanin 'yan Ingila ya yanke kowa kafin ya jefa a raga, kuma kwallon mafi tasiri a gasar cin kofin duniya da dan wasa ya yi rawarsa ya kuma yi kidarsa. Tsohon Alkalin wasan ya ce lallai shi kansa ya samu shakku a zuciya lokacin da Maradona ya jefa kwallon a raga, amma ya ce masu taya shi alkalanci sun ce kwallon babu laifi. Ali Bin Nasser dan shekaru 72 da haihuwa ya ce ya yi alkalanci wasannin mafiya wahala a tsawon rayuwarsa.

A wasannin Bundesliga na Jamus

Fußball Bundesliga 1. FSV Mainz 05 v TSG Hoffenheim
Wasannin Bundesligar JamusHoto: Alex Grimm/Getty Images

Leipzig 2  Arminia  1. Union Berlin  3 Eintracht Frankfurt  3. Augsburg 1 Freiburg 1 . Stuttgart    1 Bayern Munich  3 . FC Kolon ta bi Borussia Dortmund ta doke ta biyu da daya, muka gabatar muku wanda aka tashi, inda Lateefa Mustapha Ja'afar da Abdullahi Tanko Bala gami da Zaharren Umar Dutsen Kura suka gabatar.

A teburin na Bundesliga:

  1.  Bayern München 22
  2.  Leipzig                20
  3.  Leverkusen        19
  4.  Dortmund           1

Kokowar gargajiya a Nijar

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar, hukumar kula da wasannin motsa jiki ce da kungiyar kokowar gargajiya suka kamalla tankade da rereyen yan wasan da zasu wakilci jahar a gasar cin takobi karo na 42 da zata gudanar a Birnin Yamai.