1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 24.12.2018

Mouhamadou Awal Balarabe
December 24, 2018

Borussia Dortmund na ci gaba da cin karenta babu babbaka a teburin Bundesliga. Yayin da kungiyoyi suka tabuka abin a zo a gani a lig din Afirka kan abokar hamayyarsu a gasannin zakaru da na kalubale a Afirka.

https://p.dw.com/p/3AavP
Deutschland Borussia Dortmund v Borussia Moenchengladbach - Bundesliga | Götze und Reus
Hoto: Getty Images/Bongarts/L. Baron

Kungiyoyin kwallon kafa da ke rike da kambun zakaru na kasashen Afirka da wadanda suka lashe kofi sun gudanar da zagayen karshe na wasannin cancantar shiga rukunoni daban-daban da aka saba tsarawa. Akasarin wadanda aka saba damawa da su ne suka yi nasarar cire wa kansu kiste a wuta, irinsu Esperence ta Tunisiya da ke rike da kofin Champions lig na Afirka, da al Ahly ta Masar da ta yi fice a fannin lashe kofin zakarun Afirka.

A bangaren kofin kalubale na wadanda ke rike kofin kasashensu da aka fi sani da Confederation Cup kuwa, kungiyoyin da suka haye za su kece raini ne da wadanda suka sha kashi a wasan karshe na share fage hayewa rukuni na gaba da gasar zakaru. Sabaoda haka Coton sport ta Garoua Kamaru za ta kasance a wannan sahu bayan da ta kasa kai labari a gasar zakaru. Yayin da Ac Coton ta Chadi ta kasa kai labari, Ashante Kotoko ta Ghana kuwa ta doke Kariobangi Sharks ta (Kenya) 2-1, lamarin da ya bata damar hayewa.

Kungiyar da ta fito daga Najeriya daya tilo wato FC Rangers ce ta taka dahir a Confederation bayan da ta yi nasarar lallasa – US Madinat Bel Abbes ta (Algérie) da 2-0, lamarin da ya sha bambam da shekarun bayan, inda kulob-kulob na Najeriya suka kasance a sahun wadanda suka fi haskawa a fagen kungiyoyin gasannin Afirka.

UAE Luka Modric im Club-WM-Finale gegen Al Ain
Hoto: Reuters/A. Boyers

Kamar yadda aka hasashe tun da farko, kungiyar Real Madrid ta lashe kofinta na uku a gasar manyan kulob da ke rike da kofin zakaru na nahiyoyinsu da ta gudana a Abu dhabi. Wannan nasara da ke zama irinta na uku da ta samu a cikin tarihinta ya sa kulob din babban birnin Spain zama ja gaba a wannan fanni tun da ba wanda ya kama kafarta.

A Jamus inda aka gudanar da wasannin mako na 17 kuma na karshe na Bundesliga a wannan shekara ta 2018. Daya daga cikin wasannin da suka fi daukar hankali shi ne karon batta da abokan gaban juna suka yi wato Borussia Dortnund da Borussia Monchengldbach. Ita Dortmund da ke kan teburi ta yi nasarar huce takaicinta a kan Monchengladbach da ci biyu da daya, mako guda bayan dibar kashinta a hannun kurar baya Fortuna Düsseldorf da makamancin wannan sakamako.

A wasan da Bayern Munich ta yi da Frankfurt kuwa, Franck Ribery ne ya zura kwallye biyu daga uku da ta zura ba tare da Frankfurt ta rama ko da guda ba. Sai dai Bayer Leverkusen da ke a matsayi na tara a Bundesliga a yanzu ta kori mai horaswarta Heiko Herrlich duk da nasarori hudu da ya samu a wasanni biyar na baya-bayannan. Sai dai daraktan da ke kula da harkokin wasanni na wannan kungiyar ya zargi Herrlich da rashin tabuka abin kirki.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani