1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Labarin Wasanni: 13.06.2022

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
June 13, 2022

Dan Rasha ya zama zakaran kwallon tennis na duniya a yayin da Erling Haaland ya cimma yarjejeniyar buga kwallo a Kungiyar Manchester City ta Ingila.

https://p.dw.com/p/4CdmZ
Wimbledon I Daniil Medvedev
Zakaran gasar tennis Daniil Medvedev na kasar RashaHoto: John Walton/empics/picture alliance

Dan wasan Tennis din nan dan asalin kasar Rasha Daniil Medvedev ya sha kan zakaran wasan Tennis din na duniya Novak Djokovic. Manchester City ta kammala cinikin dan wasan nan dodon raga na Kungiyar Borussia Dortmund wato Erling Haaland a kan makudan kudi, a daidai lokacin da fitattun tsofaffin 'yan wasan kwallon kafa na Dortmund ta Jamus din, ke ziyara a kasar Ghana.

Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa na Borussia Dortmund waton Erling Haaland ya bayyana cewa a yanzu haka ya samu kansa a wajen da ya dace domin ya cika burinsa. Haaland ya bayyana hakan ne, bayan da ya sanya hannun kan yarjejeniyar komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke kasar Ingila a kan zunzurutun kudi Fam miliyan 51 da dubu dari biyu, kwatankwacin Euro miliyan 60 ko kuma Dalar Amirka miliyan 63.

Fußball Bundesliga Borussia Dortmund - SC Freiburg
Erling Haaland ya koma Manchester CityHoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

Mai shekaru 21 a duniya, yayin da yake murza leda a kungiyar ta Borussia Dortmund a Jamus, Haaland ya zura kwallaye 86 a wasanni 89 da ya bugawa kungiyar, abin da ya sanya zai shiga kungiyar ta zakarun gasar Premier League ta Ingila a bana a matsayin guda daga cikin 'yan wasan gaba da ake ji da su. A jawabinsa bayan cimma yarjejeniyar, Haaland da ke zaman da ga tsohon kyaftin din Manchester City wato Alf-Inge da ya fafata a kungiyar a shekarun 2000 da 2003 ya bayyana cewa wannan rana ta kasance abin alfahari gare shi da kuma iyalansa. Kammala sayen dan wasan, ya kawo karshen neman wanda zai maye gurmin maciyin kwallo na City Sergio Aguero dan asalin kasar Ajantina, wanda ya koma Barcelona a watan Yunin 2021.

Tsohon daraktan kudi na Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Markus Kattner zai bayar da shaida a shari'ar da ake yi wa tsohon shugaban hukumar ta FIFA Joseph Blatter da kuma tsohon shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai UEFA Michel Platini. Kotun hukunta masu manyan laifuka da ke Bellinzona a kasar Switzerland, ta tabbatar da cewa Kattner zai bayar da shaida a rana ta biyar ta sauraron shari'ar. Ana dai zargin Blatter da Platini kan yin zamba cikin aminci da sunan hukumar ta FIFA, a wata badakalar kudi kimanin miliyan biyu na kudin kasar ta Switzerland a shekarun 1998 da kuma 2002. Mutanen biyu dai sun musanta zargin da ake musu kan wannan badakala.

Joseph S. Blatter und Michel Platini
Joseph S. Blatter da Michel Platini Hoto: GES-Sportfoto/picture-alliance

Shahararren dan wasan Tennis din nan dan asalin kasar Rasha Danil Medvedev ya zamo na daya a jadawalin kwararrun 'yan kwallon Tennis na duniya, inda ya maye gurbin Novak Djokovic makwannin biyu gabanin gasar Wimbledon da aka amince ya fafata a cikinta. A baya dai Wimbledon din ta bi sahun sauran takwarorinta hukumomin kula da wasannin, inda ta harmatawa 'yan wasan Rasha da na Belarus fafata a kowacce irin gasa Sakamakon mamayar da Rashan ta yi a Ukraine. Sai dai yanzu wannan mataki da ta dauka na bai wa Medvedev mai shekaru 26 a duniya da ma, zai kara nisan ratar makin da ke tsakaninsa da Djokovica dan kasar Sabiya da ke rike da kambu. A yanzu haka dai Djokovic ya sauka zuwa mataki na uku, yayin da Alexander Zverev ke a mataki na biyu. Wannan dai shi ne karo na farko tun a watan Nuwamba na shekara ta 2003 da ya kasance shararrun 'yan wasan na Tennis wato Djokovic da Rafael Nadal da Roger Federer ko kuma Andy Murray ba su samu damar darewa mataki na daya da na biyu ba.

Formel 1 | Pirelli Grand Prix von Spanien
Gwanin tseren mota Lewis Hamilton Hoto: Hasan Bratic/picture alliance

Shahararren dan tseren motar nan na duniya Lewis Hamilton ya ce zai shiga gasar tseren motoci da za a gudanar a kasar Kanada, inda ya ce, ba zai taba bari ta wuce shi ba duk kuwa da ciwon da ya ji a gasar da aka gudanar a Baku a karshen mako. Hamilton dan asalin kasar Ingila, ya bayyana cewa, ya damu matuka da gasar da ke tafe wacce ya bayyana a matsayin tsere mafi wahala a tarihinsa. Hamilton wanda ya kasance zakaran tseren motoci na duniya har karo bakwai, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa duk da ciwon da ya ji yana hanyarsa ta haduwa da sauran 'yan tserensu domin fafatawa a gasar da ke tafe.