1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 10.10.2022

Suleiman Babayo M. Ahiwa
October 10, 2022

A karshen makon jiya ne aka raba rukunan kasashen Turai da za su kara a wasannin tantance zuwa gasar cin kofin kwallon kafar kasashen nahiyar. Akwai ma wasu fannonin wasannin.

https://p.dw.com/p/4I0TI
'Yan wasan Leverkusen suna murnar zura wa Schalke 04 kwallaye
'Yan wasan Leverkusen suna murnar zura wa Schalke 04 kwallayeHoto: Kai Pfaffenbach/REUTERS

A karshen wannan makon aka fitzar da jadawalin wasannin tantanace kasashen da za su halarci gasar neman cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Turai ta shekara ta 2024 da Jamus za ta dauki nauyi. Karkashin jadawalin kasashe biyu daga cikin wadanda suka yi fice a fagen kwallon kafa na Italiya da Ingila sun kasance karkashin rukuni guda na C, sauran kasashen rukunin su ne Ukraine, Macedoniya ta Arewa da Malta. Kasar Spain da Scotland gami da Norway suna rukunin farko na A, sannan Faransa da Netherlands suna rukuni na biyu na B.

A wasannin Lig-Lig na Jamus ake kira Bundesliga na karshen makon, kungiyar Bochum ta doke Frankfurt ci uku da nema, kana Augsburg da Wolfsburg sun tashi kunnen doki 1 da 1, yayin da Dortmund da Bayern Munich suka tashi 2 da 2. Ita ma Mainz da Leipzig sun tashi kunnen doki ne 1 da 1. Sannan Mönchengladbach ta yi raga-raga da FC Kolon 5 da 2. Wasan da Bayer Leverkusen ta lallasa Schalke da ci 4 da neman muka kawo muku kai tsaya ta rediyo, wanda Abdul-raheem Hassan da Abdullahi Tanko Bala suka jagoranta.

Sabon kocin 'yan wasan Leverkusen, Xabi Alonso yana nuna gamsuwa
Sabon kocin 'yan wasan Leverkusen, Xabi Alonso yana nuna gamsuwaHoto: Roberto Pfeil/AFP/Getty Images

A wasu daga cikin wasnnin lig na Ingila na Premier da aka kara, Manchester City da doke Southampton 4 da nema, sannan Newcastle ta yi wa Brentford cin kacar tsohon keke rakacau 5 da 1, ita ma Chelsea ta yi raga-raga da Wolverhampton 3 da nema. Sannan Manchester United ta bi Everton har gida ta doke ta 2 da 1. Arsenal ta samu galaba kan Liverpool 3 da 2. Kana a La Liga na Spain, Real Madrid ta bi Getafe gida ta doke ta 1 mai ban haushi, ita kuma Atletico Madrid ta doke Girona 2 da 1. Kan Barcelona ta doke Celta da ci 1 mai ban haushi.

'Yan wasan kungiyar Rivers United na Najeriya, za su samu tukwicin kimanin dalar Amirka dubu 40 kowanne, idan suka samu nasara a rukunin gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka wajen doke mai rike da kambun kungiyar Wydad Casablanca ta kasar Moroko. Gwamnan jihar ta Rivers, Nyeson Wike ya tabbatar da haka, wanda kuma tun farko ya ba da tukwici ga 'yan Rivers United inda kowane dan wasa ya samu dalar Amirka dubu 20 saboda lashe wasan Lig na Najeriya.

Kasar Saudiya ta yi nasarar samu damar daukan bakuncin gasar wasannin motsa jikin kasashen Nahiyar Asiya da za a gudanar a shekara ta 2029, gasar da kasar ta Saudiya ta ce za ta shirya ta a katafaren birnin nan na Neom da take ginawa a Hamadar da ke gaba da kogin Maliya, wanda ake wa lakabi da Aljannar Duniya.