1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 05.12.2022

Lateefa Mustapha Ja'afar M. Ahiwa
December 5, 2022

Fatan kasashen Afirka na kaiwa zagaye na gaba a gasar kwallon kafa ta duniya da ke yi a Katar ya fara rushewa, bayan da Ingila ta kora Senegal gida. Ko me ya rage wa nahiyar?

https://p.dw.com/p/4KUP9
Vincent Aboubakar na kasar Kamaru
Vincent Aboubakar na kasar KamaruHoto: Dylan Martinez/REUTERS

Kamar yadda ba za akasa sani ba, murna ta fara komawa ciki ga nahiyar Afirka, bayan da kasa daya tilo ta rage cikin kasashe biyar da ke wakilitar nahiyar a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ke gudana a Katar. Hakan dai ta faru ne bayan da Ingila ta caskara Senegal da ci uku da nema a zagayen kwaf daya na 'yan 16. A yanzu dai Maroko ce ta rage ga kasashen Afirkan, inda za ta fafata da Spain a gobe Talata da misalin karfe hudu agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi karfe uku ke nan agogon GMT da Ghana. Ita dai Senegal ta buga wasan ne babu fitaccen dan wasanta Sadio Mane sakamakon ciwon da ya ji a kafarsa daf da fara gasar. Rabon Senegal ta kai wannan mataki na kwaf daya dai, tun a shekara ta 2002.  

Mai horar da 'yan wasan kasar Senegal, Aliou Cissé
Mai horar da 'yan wasan kasar Senegal, Aliou Cissé Hoto: Ozan Kose/AFP

Ba dai Senegal ce kadai kasar da aka kora gida a zagayen na kwaf daya ba, domin kuwa a ranar Lahadi Faransa ta kora kasar kasar Poland gida bayan ta lallasa ta da ci uku da daya. A ranar Asabar din karshen mako kuwa, Argentina ta fattaki Australia gida da ci biyu da daya. Haka kuma ta kasance a karawar Holland da Amirka, inda Amirkar ta hada kayanta zuwa gida bayan ta sha kashi da ci uku da daya. Tun dai daga shekarar 1994 ne Amirka ta fara samun nasarar shiga cikin kasashen yankin da za su halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

Ya zuwa gasar bana da ake fafatawa a kasar Katar, Amirkan ta samu halartar gasar har sau takwas a kasashe dabam-dabam da suka hada da Faransa da Jamus da Koriya ta Kudu da Brazil da Afrika ta Kudu. Sai dai in ban da a Koriya ta Kudu da Amirkan ta kai wasan dab da na kusa da na karshe wato quarter finals, ba ta taba wuce matakin na kwaf daya mai kasashe 16 ba kamar yadda tarihi ya sake maimaita kansa a bana.

A wannan Litinin, Japan za ta kara da Crotia kana Brazil ta fafata da Koriya ta Kudu. A ranar Talata Maroko za ta kece raini da Spain, kana Portugal ta gwabza da Switzerland. A ranar Jumma'a tara ga wannan wata na Disamba, za a fara buga wasannin dab da na kusa da na karshe, inda Holland za ta fafata da Argentina. A ranar Asabar 10 ga wata kuma, Ingila ta gwabza da Faransa. Sannan a ranakun 13 da 14 a fafata a wasannin kusa da na karshe wato Semi finals kana a fafata a wasan neman zama na uku a ranar Asabar 15 ga watan na Disamba. Za dai a kammala gasar a ranar 18 ga wannan wata na Disamba da muke ciki.

Opening Ceremony - Beijing 2022 Winter Olympics Day 0
Hoto: Julian Finney/Getty Images

Akwai yiwuwar Saudiyya ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Asiya da za a yi a shekara ta 2027, bayan da Indiya ta janye daga takarar karbar bakuncin. Da ma dai Indiya da Saudiyya ne kawai ke takara, abin da ya sanya janyewar Indiyan ke zama dama ga Riyadh din ta karbar bakuncin gasar.

Saudiyya dai ba ta taba daukar nauyin gasar da kasar ta lashe har sau uku a ba. Koda yake rahatoanni sun nunar da cewa kasar na fatan karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a shekara ta 2030, duk da gaza tsallake matakin rukuni da kasar ta yi a gasar da ake fafatawa a yanzu a makwabciyarta Katar. A wani labarin kuma, Katar din ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Asiyan ta shekara ta 2023 da ke tafe, bayan da China ta janye kudurinta na shirya gasar sakamakon tsaurara matakan yaki da annobar Corona da ta addabi duniya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani