1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaJamus

Labaran Afirka masu daukar hankali a jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 23, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta samu damar sake kai kayan agajin jin-kai daga Chadi zuwa yankin Darfur na Sudan da yunwa tai wa katutu.

https://p.dw.com/p/4jqPM
Hoto: ALI SHUKUR/AFP

Za mu fara da jaridar die tageszeitung a sharhinta mai taken: Ayarin motocin kayan abinci sun isa Darfur, a karshe Majalisar Dinkin Duniya ta samu damar sake kai kayan agajin jin-kai daga Chadi zuwa yankin Darfur na Sudan da yunwa tai wa katutu. A karkashin tsarin nan na bayar da damar kai kayan agajin jin-kai, a baki dayan Sudan din. Jaridar ta ce: A karon farko tun tsawon watanni, kayan agajin jin-kai sun isa yankin Darfur da yaki ya daidaita daga makwabciyar kasa Chadi. A Yammacin Talatar da ta gabata, ayarin motoci dauke da kayan agajin jin-kai na Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya isa kan iyakar Sudan da Chadi ta Adré da ke da matukar muhimmanci.

Sudan | Vorsitzender des Souveränen Rates des Sudan | Abdel Fattah al-Burhan
Abdel Fattah al-BurhanHoto: AFP

Tun bayan da a makon da ya gabata gwamnatin mulkin sojan Sudan din ta sanar da bayar da damar bude iyakar ta Adré, ayarin motocin kayan agajin biyu makare da kimanin ton 6.000 domin mutane dubu 500 suka shirya tsab da nufin kai dauki. Cikin watan Afrilun shekarar 2023 da ta gabat ne dai, yaki ya barke a yankin na Darfur na Sudan din tsakanin sojojin gwamnati karkashin jagorancin shugaban kasa na mukin soja Abdelfattah al-Burhan da kuma mayakan rundunar RSF karkshin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo da aka fi sani da Hametti. Yakin dai ya halaka mutane da dama, inda kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa kimanin mutane miliyan 13 daga Sudan din na gudun hijira.

Birkin dole: Adadin al'ummar Arewacin Afirka da ke kasada da rayuwarsu zuwa Italiya ta hanyar Tekun Bahar Rum ya ragu matuka, hakan ya doru ne a kan Tunusiya da Libiya in ji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ce wani abu ya sauya a wannan barazarar a Italiya, tsawon shekaru dubban bakin haure ne ke kwarara Turai ta hanyar Tekun Bahar Rum din da ya sanya masu bayar da agaji ke aiki tukuru. Batun ya zama ruwan dare a cibiyoyi da dama, tare da zama babu abin tattaunawar da ya fishi a kafofin yada labarai da kuma tsakanin 'yan siyasa.

Libyen Tunesien Migration
'Yan gudun hijira a TunisiyaHoto: MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images

Wata majiya daga Italiya ta bayyana cewa ya zuwa ranar 19 ga wannan wata na Agusta da muke ciki adadin bakin hauren ya ragu matuka, inda ma'aikatar harkokin cikin gidan Italiyan ta ce mutane dubu 38 ne kacal suka isa kasar ta hanyar teku a bana. A shekarar da ta gabata a daidai wannan lokaci, adadain ya kai dubu 105, wanda kuma ya nunka haka a shekara ta 2022. Jaridar ta ce: ana tura makudan kudi zuwa Tunis da Tripoli, domin hana bakin hauren karasawa Turai. Wannan na kunshe karkashin wani shiri da aka kaddamar a shekarar da ta gabata ta 2023, inda kungiyar Tarayyar Turai EU ta shaidawa Tunisiya za ta bata kudi har Euro miliyan 105.

Ba mu karkare da jaridar die tageszeitung a sharhinta mai taken: Fitaccen dan siyasar Afirka ta Kudu ya sake yin karkon kifi, tsohon shugaban kasa Jacob Zuma ya taka rawar gani a zaben da ya gabata a karkashin jam'iyyarsa ta MK. Sai dai watanni uku bayan nan, ya sake tarwatsa kansa. Amma kuma takwarorinsa na jam'iyyar masu ra'ayin gaba-dai-gaba-dai, suma ba sa taka wata rawar azo a gani. A yayin zaben majalisar dokokin Afirka ta Kudun da ya gudana a watan Mayun wannan shekarar, jam'iyyar Zuma ta MK ta bayar da mamaki ta hanyar zuwa matsayi na uku bayan kammala kidaya kuri'un da aka kada.

Südafrikas ehemaliger Präsident Zuma | Beitritt der MK-Partei zu einer Anti-ANC/DA-Oppositionskoalition
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ZumaHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Jam'iyyar ANC da ta kwashe shekaru 30 tana mulki a kasar, ta rasa rinjayenta a karon farko. Hakan ya tilasta mata kafa gwamnatin hadaka da jam'iyyar AD, yayin da MK da sauran kananan jam'iyyu suka zama manya a bangaren adawa. Sai dai a yanzu, Zuma na jagorancin jam'iyyar ta MK ta hanyar kama-karya da nufin daukar fansa a kan tsohuwar jam'iyyarsa ta ANC ba wai domin kawo sauyi ko ci-gaba a kasar ba.