Labaran Afirka da suka fito a jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 24.02.2023
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Labaran Afirka da suka fito a jaridun Jamus

Hankalin jaridun na Jamus a wannan makon ya karkata zuwa kan babban zaben Najeriya da taron AU da kuma kudirin Jamus na daukar kwararru a Ghana.

Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Neue Zürcher Zeitung

Babban zabe kuma mafi muhimmanci. Wannan shi ne taken sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta yi tsokaci kan zaben Najeriya da zai gudana a gobe Asabar inda yan Najeriyar miliyan 93 da za su kada kuri'a kuri'a.

Jaridar ta ce kasar ta yammacin Afirka ita ce mafi karfin tattalin arziki kuma mafi yawan al'umma a nahiyar da mutane sama da miliyan 200. Ta ce nan da shekaru 30 masu zuwa Najeriya za ta zama kasa ta uku mai yawan jama'a a duniya bayan India da China inda za ta sha gaban Amurka.

Ta ce Najeriya muhimmiyar kasa ce kuma darajarta zai kara habaka. A yanzu za ta gudanar da zaben da aka dade ba a gani ba a Afirka. Mutane miliyan 93 da suka yi rajista za su fito domin zaben shugaban kasa. Idan daya daga cikin yan takara 18 da ke neman kujerar shugabancin kasar ya yi nasara a zagayen farko da rinjayen fiye da kashi 50 cikin dari na kuri'iun da ake bukata.

Zaben yana da muhimmanci saboda Najeriya ita ce kan gaba da dadi ba dadi. Ci gaban dimukuradiyya da daidaiton tattalin arziki a kasar zai jagoranci daukacin yankin ko ma gaba da haka. To amma rashin kwanciyar hankali ko tangal tangal na iya yin barazana ga makwabtanta.

Masu zabe a Port Harcourt

Masu zabe a Port Harcourt

Frankfurter Allgemeine Zeitung

 

Abin kunya ga Israila a taron kungiyar gamaiyar Afirka AU.

Jaridar ta ce a taron koli na shekara shekara na shugabannin kungiyar tarayyar Afirka, an yi badakala da ya kunyata Israila. A yayin bude taron a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, an kori tagawar Israila daga zauren taron. Jaridar ta ce wani faifan bidiyo ya nuna jami'ai da dogarai suna raka jami'ar Israila Sharon Bar-Li wadda mataimakiyar darakta ce mai kula da Afirka a ma'aikatar harkokin wajen Israila.

Daga bisan wata mai magana da yawun kungiyar tarayyar Afirka ta ba da dalilin cewa jami'ar ba ta da takardar tantancewa ta halartar taron shi ya sa aka fidda da ita kuma tuni suka sanar da jakadan Israila a kasar Habasha.

Israila wadda tsawon shekaru ke fatan samun matsayin 'yar kallo a kungiyar tarayyar Afirka ta baiyana takaici da cewa kungiyar ta bar kasashe kamar Afirka ta kudu da Algeria da Iran wadanda kiyayya ta yi musu katutu su juya akalarta.

Shugaban Afirka ta Kudu Syril Ramaphosa ya bukaci Israila ta bada cikakkiyar kan zargin da ta yi. wata sanarwa ta ce Israila ta yi kokari na yin kafar ungulu ga muhawarar da aka so yi kan wani rahoto da ya shafi ba ta matsayin 'yar kallo a kungiyar. A shekarar da ta gabata kungiyar tarayyar Afirkar ta dage kada kuri'a kan kudirin domin kauce wa sabani a cikin kungiyar mai mambobin kasashe 55. A maimakon haka kafa kwamiti domin duba batun. Cikin kasashen da ke adawa da karbar Israila a matsayin 'yar kallo a kungiyar sun hada da Algeria.

Taron kungiyar AU a Addis Ababa

Taron kungiyar AU a Addis Ababa

Der Tagesspiegel

Jaridar der Tagesspiegel ta rubuta sharhinta ne akan kudirin Jamus na dauko kwararrun ma'aikata daga Ghana.

Jaridar ta ce a lokacin ziyararta a Ghana ministar raya kasa ta Jamus Svenja Schulze da ministan kwadago Hubertus Heil sun kaddamar da shirin dauko kwararrun ma'aikatan daga Ghana inda Heil yace samun kwararrun ma'aikatan zai habaka nasarori da ci gaban Jamus. Ita ma ministar raya kasa Svenja Schulze ta baiyana manufar kaurar jama'a da manufar raya kasa wadanda ta ce suna da dangantaka da juna kuma abu ne da zai taimaki tattalin arzikin kasashe aminan juna musamman ga Jamus da ke fama da karancin kwararrun ma'aikata.

Jaridar ta ce rashin aiki na matasa a kasa kamar Ghana za su sami mafita ta hanyar kawancen kasashen biyu. A waje guda kuma kwararrun da suka yi kaura za su taimakawa kasar su ta hanyar tura kudi gida da kuma karfafa musayar ilmi da fasaha.

 Svenja Schulze da Gilbert F. Houngbo da Hubertus Heil

Svenja Schulze da Gilbert F. Houngbo da Hubertus Heil

die Tageszeitung

A nata bangaren Jaridar die Tageszeitung ta yi tsokaci ne kan yadda damunar bana a kudancin Afirka ta jefa kasar Malawi cikin kangin sauyin yanayi da matsalolin lafiya.

Jaridar ta ce ana kukan targade sai ga karaya ta zo. Bayan tsawon shekaru da dama ana fama da matsalar sauyin yanayi sai ga shi a damunar bana an sami ambaliya mafi muni da kasar ta gani a tarihi. An sami barkewar cutar kwalara da aka dade ba a gani ba a kasar. malawi na daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya.

Jaridar ta ce kudu maso gabashin Afirka na cikin yanayi mawuyaci ga matsalolin sauyin yanayi sannan ga annobar kwalara da ake samu sakamakon gurbacewar ruwan ko abinci. Daga farkon wannan watan kadai mutane kusan 7,000 suka kamu yayin da mutum 239 kuma suka rasu kuma yawanci a babban birnin kasar ta Malawi Lilongwe da kuma Blantyre babbar cibiyar kasuwanci. Kididdigar da gwamnatin ta bayar a ranar litinin ya nuna mutane fiye da 42,000 suka kamu da cutar yayin da fiye da 1,300 kuma suka rayu tun bayan barkewar annobar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin