1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labaran Afirka da ke jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
February 10, 2023

Rikicin yankin gabashin Kwango da kashe mayakan Al Shabaab a Somaliya na cikin jaridun Jamus na wannan mako.

https://p.dw.com/p/4NM0l
Somalia Militants Twitter
Hoto: picture alliance / AP Photo

Bari mu fara sharhin jaridar die Tageszeitung wacce ta ce harbin kisa daga sojojin MDD. Jarida ta ci gaba da cewa, bayan kwanaki da dama na zanga-zangar adawa da dakarun shiga tsakani na kasa da kasa a yankin gabashin Kwango, mutane biyar sun mutu a arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da dakarun kiyaye zaman lafiya na Monusco a gabashin kasar.

An yi imanin wasu mutane biyar da yaki ya raba da muhallansu, dakarun Majalisar Dinkin Duniya suka harbe har lahira. Akalla wasu mutane takwas sun jikkata, a cewar Iduma Molengo, shugaban ‘yan sanda na Nyagongo da ke gefen arewacin Goma babban birnin lardin.

A sharhinta jaridar Der Tagesspiegel ta ce "Abu ne mai nauyi ga masu kishin Islama". Mayakan Al Shabaab makonni biyu da suka gabata an kashe masu mayaka masu yawa. Dakarun Somaliya sun kama mayakan jihadi a lardin Shabeellaha Hoose da ke kudanci. Karin sojoji sun kai farmaki kan mayakan Al-Shabaab mai yiwuwa su biyo baya a cikin makonni da watanni masu zuwa.

Gwamnatin Somalia a yanzu tana fatan taimako gada kasashe makwabta. A wani yunkurin na neman goyon bayansu, shugaba Hassan Sheikh Mohamud a makon da ya gabata ya gayyato takwarorinsa na Kenya, Habasha da Djibouti zuwa babban birnin Mogadishu.  Tare suna son daukar abin da suka kira  "mataki na karshe" don zama cikakke kawar da al-Shabab a Somaliya baki daya.

Sai Frankfurter Allgemeine Zeitung wa ce ta ce "Gwamnatin Aljeriya na murkushe masu sukar ta tare da kara tsanantawa. Kungiyar kare hakkin dan Adama mafi dadewa wace aka kafa a shekara ta 1985 Algerian League for the Defence of Human Rights (LADDH) na cikin masu fuskantar fushin gwamnati.  Kungiyar da tun daga lokacin ta fara adawa da danniyar mahukunta, ta yi yakin neman 'yancin 'yan adawa, da kuma 'yan tsiraru na yin zanga-zangar.