Kyuba ta tura likitotci yaki da Ebola | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kyuba ta tura likitotci yaki da Ebola

Likitocin Kyuba sun isa Laberiya domin yaki da cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka

Wani jirgin sama dauke da likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya kimanin 50 na kasar Kyuba, wadanda za su yi jinya masu cutar Ebola, ya dauka a kasar Laberiya.

Jirgin mallakin kasar ta Kyuba ya isa kasar cikin taimakon da kasashen duniya ke bayarwa wajen yaki da cutar Ebola a kasashen yankin yammacin Afirka. Akwai wasu likitoci 40 da za su isa kasar Gini. Kasar ta Kyuba tana cikin kasashen duniya da suka tura likitoci da ma'aikatan lafiya domin tabbatar da dakile cutar Ebola. Kasashen Amirka, da Birtaniya da Faransa gami da Jamus suna ci gaba da tura ma'aikatan lafiya domin tunkarar cutar ta Ebola.

Alkaluman hukumar Lafiya ta Duniya sun nuna cewa fiye da mutane 4500 cutar ta hallaka, yayin da ta kama kusan mutane 10000.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba