Kwashe ′yan kasar waje daga Afirka ta Tsakiya | Siyasa | DW | 18.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwashe 'yan kasar waje daga Afirka ta Tsakiya

Kasar Kamaru ta fara kwashe 'yan kasarta dake makwabciyarta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da ta tsunduma cikin rikicin addini.

Kasar kuma na kai kayan abinci ga sauran 'yan Kamarun da basa son komawa gida, yayin da a tashar jiragen ruwa dake Duala kaya na nan jibge sakamakon kin daukarsu zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da masu manyan motoci suka yi. Jirgen sama na musamman guda biyu kasar Kamaru ta tura domin kwaso 'yan kasarta dake Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar a bisa umarnin shugaban kasar Paul Biya. Daya daga cikin jiragen dai ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake Bangui babban kasar da 'yan kasar ta Kamaru kimanin 300 domin maida su gida.

Neman agajin gwamnati daga 'yan kasar.

Dubun dubatar 'yan Kamaru dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne dai, suka bukaci gwamnatinsu da ta kai musu dauki domin kwaso su daga kasar da rikicin addini ke neman dai dai tawa. Kiran da jakadan Kamaru a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ya bayyana da cewa ya zama wajibi, domin kuwa babu damar yin amfani da hanyoyin mota domin kwaso su daga kan iyakokin kasashen biyu.


Ya ce "Mutanen sun yi kokarin daukar hayar manyan motoci domin su kwaso su zuwa Garoua Boulaye, inda suka bukace ni da in taimaka musu in basu sojan da zai musu rakiya zuwa can. Abu ne mai matukar wahala mu iya yin hakan a dangane da haka na ce su zo ofisjhin jakadancin Kamaru".

Dubban 'yan kasar ta Kamaru dai sun amsa kiran jakadan nasu, yayin da wasu suke kokarin kai kansu zuwa ofishin jakandancin nasu dake Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar. Ga dai yadda wasu 'yan Kamaru da suka shafe shekaru a Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar ke bayyana yadda lamarin yake.

Yace: "A yayin da aka kawo gawar wani Musulmi masallaci, sai hankula suka tashi, inda suma suka fara kashe Kiristoci. An kashe 'yan Senigal da 'yan Sudan da 'yan Mali kai duk dai wadanda suke 'yan kasashen ketare, an kashe 'yan Kamaru da dama a kan idona. Wanna kuwa dake zaman malamar jinya cewa take: " Sun karkashe mutane a gabanmu, sun aikata manyan laifuka a kansu da suka hadar da kwace wa mutane kayansu da kuma yi musu fyade harma da sace su".

Tsofaffin 'yan tawayen Seleka na muzgunawa 'yan Kamaru

Rahotanni dai na nuni da cewa harkokin kasuwanci da tattalin arziki sun tsaya cak a Jamhuriyar Afirka ta TSakiyar. Wadannan wasu 'yan Kamaru ne da suka shaidar da cewa sun watsar da sana'oinsu sakamakon muzgunawar da 'yan tawayen Seleka ke yi musu bisa zarginsu da zama 'yan leken asirin tsohon hambararren shugaban kasar Farncoise Bozize.

Yace: "Yan tawayen Seleka sun kama ni tare da buguna a cikin daji inda suka kwace min komai nawa suna masu cewa mu 'yan Kamaru muna yiwa Bozize leken asiri ne". Ita kuwa wannan cewa ta yi "Magoya bayan Shugaba Michel Djotodia na yawan kaiwa 'yan Kamaru dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya farmaki, bisa zargin da sukewa Kamaru na goyon bayan hambararren tsohon shugaban kasar Francoise Bozize".

Baki dayan 'yan Kamarun da suka sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Douala a Kamarun na cikin farin ciki da annashuwa bisa cetosu da suka ce gwamnatin kasar su ta yi. Kasar Kamaru dai ta bawa Bozize mafaka tun bayan da ya tsere daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakamakon juyin mulkin da 'yan tawayen Seleka suka yi masa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh