Kwango: Za a takaita yaki da Ebola | Labarai | DW | 16.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango: Za a takaita yaki da Ebola

Kungiyar gajin kasa da kasa ta Red Cross ta yi gargadin takaice ayyukan yaki da cutar Edola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a makonni masu zuwa a bisa dalilin rashin kudi

Kungiyar agaji kasa da kasa ta Red Cross ta yi gargadin cewa matsalar rashin kudi na barazanar cilasta mata takaice ayyukanta na yaki da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a makonni masu zuwa a daidai lokacin da adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ke karuwa a yanzu haka. 

A wani taron manema labarai da ya yi a wannan Alhamis a birnin Geneva, daraktan sashen kiwon lafiya na kungiyar ta Red Cross Emanuele Capobianco ya ce yanzu haka cutar ta Ebola na kara kamari a kasar ta Kwango inda daga farkon shekara ya zuwa yanzu ta halaka mutane kusan dubu da 150 daga cikin mutun dubu da 700 da suka harbu da cutar musamman a makonni uku na baya bayan nan. 

Kungiyar ta Red Cross ta ce kawo yanzu kasa da rabi na kudin miliyan 28 na Euro da ta bukata domin tunkarar matsalar ne suka shigo hannunta.