Kwango: 'Yan adawa na shakku da shirin zabe
October 31, 2018Talla
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar tsaron kasar ta ba wa hukumar zaben kasar tankunan yaki 150 da jiragen yaki da dama a wani mataki na inganta tsaro a lokutan gudanar da zaben.
Duk da haka dai babbar jam'iyyar adawa a jamhuriyar dimukuradiyyar Kwango wato Union for Democratic and Social Progress UDPS, ta ce ba a shirya yin zabe ba kuma 'yan adawa ba su gamsu da matakan tsaro ba.
Wani zaben jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa duk da irin rikita-rikitar da ake fama kan zaben, amma 'yan takara biyu daga jam'iyyun adawa na kan gaba a takarar shugabancin kasar.