1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Tshisekedi ya yi rantsuwar kama aiki

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 24, 2019

A wannan Alhamis ne aka rantsar da Felix Tshisekedi a matsayin sabon shugaban kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan da ya lashe zaben kasar da ke cike da rudani.

https://p.dw.com/p/3C4m0
DR Kongo  Kinshasa Vereidigung Präsident Felix Tshisekedi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Kwango, Felix Tshisekedi ya yi alkawarin sakin dukkanin fursunonin siyasa tare da yaba wa mahaifinsa tshohon jagoran adawa wanda ya baiyana a matsayin gwarzo.

Tshisekedi mai shekaru 55 a duniya, ya karbi mulki daga hannun Kabila da ya kwashe shekaru 18 yana mulkin kasar bayan da ya gaji mahaifinsa Laurent-Desire wanda aka hallaka a shekara ta 2001. Koda yake dan takarar jam'iyyar adawa Martin Fayulu ya nunar da cewa shi ne ya lashe zaben da kaso 61 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yana mai bayyana sakamakon zaben da wani tsararren juyin mulki daga Kabila da Tshisekedi.

Felix Tshisekedi dai ya tabbata zababben shugaban ne, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana sahihancin sakamakon zaben da hukumar zaben kasar CENI ta bayar. 

Tuni dai tsohon shugaban kasar, Joseph Kabila ya yi kira ga al'ummar kasar da su hada kawunansu. Wannan ne dai karo na farko da gwamnatin farar hula ta mika mulki ga wata gwamnatin farar hula a tarihin Kwangon da ke da dinbin arzikin karkashin kasa, tun bayan samun 'yancin cin gashin kai daga kasar Beljiyam a shekara ta 1960.