1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SADC ta bukaci a sake kidayar kuri'u a zaben Kwango

Ahmed Salisu
January 13, 2019

Kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC ta bukaci hukumar zaben Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da ta sake kidayar kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar wanda Felix Tshisekedi ya lashe shi.

https://p.dw.com/p/3BUAo
Kongo Wahl Symbolbild
Hoto: Reuters/B. Ratner

SADC din ta mika wannan bukata ce ga Kwango a wannan Lahadin, inda ta ke cewar sake yin kidayar zai taimaka wajen kwantar da hankalin wadanda su ka yi nasara da wadanda su ka sha kaye a zaben na wata Disamabar shekarar da ta gabata.

A share guda kuma kungiyar ta bukaci 'yan sayasar kasar da su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin sun girka gwamnatin hadin kan kasa wadda za ta bada dama a yi tafiya da dukannin bangarori na siyasar kasar don a samu zaman lafiya mai dorewa.

Wannan bukata da SADC ta gabatar na zuwa ne bayan Martin Fayulu wanda ya zo na biyu a zaben na Kwango ya bukaci kotun kolin kasar da ta soke zaben baki dayansa saboda zargin tafka magudi.