Kwango: Ranar zabukan kasar na kara yin nisa | Siyasa | DW | 12.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwango: Ranar zabukan kasar na kara yin nisa

Al'ummar kasar Kwango na cigaba da mayar da martani mabmbanta dangane da dage zaben shugaban kasar da hukumar zaben ta yi domin samun isheshen lokaci.

Kongo Präsident Joseph Kabila (picture alliance/AP Images/J. Bompengo)

Shugaban kasar Kwango Joseph Kabila

Da farko dai, an dai shirya gudanar da zaben shugaban kasar na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango a cikin wasu watanni masu zuwa a wannan shekara, to sai dai hukumar zaben kasar ta fitar da sanarwar a ranar Laraba inda ta nemi akalla kwanaki sama da dari biyar nomin gudanar da cikakken shiri bayan ta kamalla kidayar masu zabe wanda kuma ya gagara kamaluwa a yankin Kasai mai fama da yake-yake.

Ranar zabe na shan dagawa a Kwango

Ita dai hukumar zaben ta Kwango ta sha dage zaben a baya, inda a watan yuli ma da ya gabata ta bayyana cewa ba za a iya gudanar da zaben gamari ba a kasar sakamakon rikici da ake fama da shi a wasu sassan kasar musamman ma  yankin kasai. Jami'an difilomasiya a Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango dai a nasu bangare sun amince da dalilai da hukumar zaben kasar ta bayar na rashin yuhuwar gudanar da zaben nan da watanni uku masu zuwa sakamakon dalilai na kayan aiki. Amma sun bayyana cewa dole hukumar ta fitar da jadawalin zaben da zai nuna wa 'yan kasar ranekun da za a gudanar da zaben ba wai hasashe ba.

Daga zabe ko neman makalewa kan mulki

Afrika Demokratische Republik Kongo - Delly Sesanga spricht zu den Medien (Reuters/T. Mukoya)

Dab adawar kasar Kwango Delly Sesanga

Sai dai kuma masu sharhi kan al-amuran siyasar kasar na ganin cewa jinkirin gudanar da zaben wani salo ne na shugaba kabila domin yin zaman dirshen a kan kujrar mulkin kasar, kamar yanda Docta Phil Clark masanin harkokin siyasa na jami'ar SOAS da ke Ingila kuma  kwararre kan harkokin siyasar kasar ta Kwango ya bayyana. Duk da cewa 'yan adawar kasar sun nuna rashin gamsuwar su da matakin na hukumar zaben Docta Phil Clark ya kara ce rashin hadin kai a tsakanin 'yan adawar kasar na haifar da karin rashin mafita game da rikicin siyasar kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin