Kwango na fatatakar ′yan tawaye | Labarai | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwango na fatatakar 'yan tawaye

Sojojin Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango sun ƙaddamar da farmaki kan 'yan tawayen Ruwanda

Gwamnatin ƙasar Jamhuriyar Demokaraɗiyyar Kwango ta ƙaddamar da hare-hare kan 'yan tawayen Hutu na kasar Ruwanda da ke gabashin ƙasar, bayan wa'adin ajiye makamai ya wuce. Gwamnatin tana zargin 'yan Ƙungiyar ta FDLR wadda ke da alhakin kisan kare dangin ƙasar Ruwanda na shekarar 1994, da haddasa fitunu na tsawon shekaru 20 a gabashin ƙasar ta Kongo Kinshasa.

Akwai dakarun kiyaye zaman lafiya a yankin waɗanda suka taimaka wajen dƙkile yaƙin basasan shekara da shekaru.